Wasu Mutane Ɗauke Da Bindigu Sun Yi Garkuwa Da Ɗanjarida a Legas
- Katsina City News
- 19 Mar, 2024
- 397
Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane dauke da manyan bindigu sun yi dirar mikiya a gidan Segun Abiodun Olatunji, tsohon shugaban ofishin jaridar The PUNCH na Kaduna, a gidansa da ke Iyana Odo a unguwar Abule Egba a jihar Legas.
Abiodun wanda a yanzu babban edita ne na jaridar FirstNews, kuma a wata sanarwar da jaridar ta fitar a ranar Asabar din da ta gabata, hukumar gudanarwar kafar yada labaran ta alakanta lamarin da wani labari na baya-bayan nan da jaridar ta FirstNews ta buga mai taken,
"Revealed: “Defence Chief running office like family business – Public Interest Lawyers”.
Labarin da ke da alaƙa da ofishin rundunar tsaro.
Sanarwar ta ce karin wasu kafafen yaɗa labarai na yanar gizo sun buga labarin.
Sanarwar ta kara da cewa ta yiwu sace ɗan jaridar na da alaƙa da wani rahoto mai taken
EXCLUSIVE: How contractor, company stole N100bn, laundered funds for top govt officials – Investigation”. Wato labarin yadda dan kwangila da wani kamfani ya saci Naira biliyan 100bn, labarin da jaridar ta goge ta kuma janye shi daga baya.
A cewar sanarwar, uwargidan ɗanjaridar , ta ce mutanen ɗauke da manyan bindigu da yawansu ya kai mutum goma sun isa gidansu ‘yan mintuna kadan bayan karfe 6 na yamma, suka tafi da mijinta ba tare da bayyana inda za su kai shi ba.
Ta ce “Wasu ‘mutane ne sanye da kakin soji sun kai goma (biyu cikinsu basa sanye da kayan soji, suna sanye da kayan guda ne,mutum 8 sanye da kayan soji, amma dukkansu dauke da makamai) sun isa gidanmu da ke titin Dauda Oriyomi, Iyana Odo a unguwar Abule Egba a jihar Legas, suka tafi da mijina".
Ta ce mijin nata yayi ta maimaita cewa, su faɗa masa laifinsa, su kuma faɗa masa inda zasu tafi da shi, amma suka ƙi faɗa masa.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton babu ɗoriyar Ɗanjaridan sama da kwanaki biyar da faruwar lamarin.