An Tsinci Gawar Hakimi a Bauchi Bayan 'Yan Bindiga Sun Sace Shi
- Katsina City News
- 18 Mar, 2024
- 671
Ana Zargin 'yan bindiga sun kashe hakimin kauyen Riruwai da ke gundumar Lame na karamar hukumar Toro a jihar Bauchi.
A ranar Litinin din da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka sace Garba Badamasi a kauyen, a ranar Juma’a kuma ba a san inda yake ba har zuwa ranar Lahadin da ta gabata inda jami’an tsaro suka gano gawar sa.
A ranar Lahadin da ta gabata ne aka kai gawar zuwa fadarsa da ke Lame inda aka yi masa sallar jana’iza kuma aka binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Alkaluma sun nuna cewa ta’addanci ya karu matuka a karamar hukumar Toro, musamman a dajin Magama Gumau, gurguzu, da dajin Bura da ke karamar hukumar Ningi, wadannan yankuna ne suka fi fama da matsalar ta’addanci a jihar Bauchi.
Madogara: Premium Times