Tinubu ya naɗa mace a matsayin shugabar NACA a karo na farko a tarihi
- Katsina City News
- 14 Mar, 2024
- 386
Shugaba na ƙasa Bola Tinubu ya nada Dokta Temitope Ilori a matsayin sabuwar Darakta-Janar ta Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Kasa (NACA), wanda hakan ke nuna wani gagarumin ci gaba da aka samu a yayin da ta zama mace ta farko a tarihi da ta rike wannan mukami.
A ranar 22 ga Fabrairu, 2024, Dokta Ilori ta hau kujerar ta ta a hukumance, na tsawon shekaru hudu, inda ta gaji Dr. Gambo Aliyu, wanda ya rike mukamin DG daga watan Yuni 2019 zuwa Fabrairu 2024.
Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin jami'in hulda da jama’a da ka’idojin hukumar ta NACA, Toyin Aderibigbe, a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yau.
Kafin nada ta, Dokta Ilori ta yi aiki a matsayin Babbar Malama a Sashen Nazarin Magungunan Jama'a na Jami'ar Ibadan da kuma matsayin mai ba da shawara kan Likitan Iyali a Sashen Kula da Magungunan Iyali a Asibitin Kwalejin Jami'ar Ibadan.