Gwamnatin Najeriya ta karɓo rancen dala biliyan 1.3 domin kammala aikin titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Maraɗi
- Katsina City News
- 14 Mar, 2024
- 532
Gwamnatin Najeriya ta karɓo rancen dala biliyan 1.3 domin kammala aikin titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Maraɗi da ke Jamhuriyyar Nijar.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya ta fitar a jiya Laraba.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa kamfanin gine-gine na ƙasar China, CCECC, ne zai samar da kaso 85 na kuɗaɗen da ake buƙata.
Haka kuma, ma’aikatar ta ce Gwamnatin Najeriya da haɗin gwiwar Bankin habaka tattalin arzikin Afirka na Africa Development Bank ne ke ɗaukar nauyin aikin.
“Samun bashin na dala biliyan 1.3 na nuna irin nasarar da za a samu wajen kammala layin dogon,” in ji sanarwar.
Wannan dai na ɗaya daga cikin shirye-shiryen Gwamnatin Najeriya na inganta harkar sufuri a faɗin ƙasar domin bunkasa tattalin arziki da ke fama da masassara