Gwamnatin jihar Zamfara ta Haramta Saida Burodi ba akan Ƙa'ida ba, tare da zubashi a cikin Buhu
- Katsina City News
- 13 Mar, 2024
- 510
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya sanya hannu a kan dokar da ta haramta sayar da biredin da ba a liƙa takardar shaidar inda ake yin sa ba, tare da jigilar sa a buhu. Haka kuma an haramta sayar da man fetur fiye da lita 50, haka ma an haramta motoci masu gilashi mai duhu a duk faɗin jihar Zamfara.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ta ce dokar mai lamba 02 da mai lamba ta 04, 2024 za ta taimaka wajen magance wasu matsalolin da ke taimakawa ga matsalar tsaro a jihar. Jiya Talata ne Gwamnan ya sanya hannu a dokar a gidan gwamnatin jihar da Gusau
Kakain Gwamnan ya ce, an sanya dokar ne sakamakon hare-haren da ake kai wa wasu al'ummomi a sassan jihar.
“Sakamakon hare-haren da aka kai wa al'ummomin wasu Ƙananan Hukumomin jihar nan, musamman Zurmi, Shinkafi, Ƙaura Namoda da Talata Mafara, tare da samun ƙaruwar kai hare-hare da sace mutane a wasu yankuna da manyan hanyoyin jihar.
“Gwamna Lawal ya sanya hannu a dokar No. 02 2024, wacce ta haramta sayar da biredi mara takardar shaida, tare da sanya biredin a buhuna, an kuma haramta wasu ayyukan da ba a amince da su ba a jihar.
“Wajibi ne duk gidajen biredi su sanya takarda mai ɗauke da cikakken adireshin kamfanin, tare da bayanan ayyukan da su ke aiwatarwa, ana so su yi wannan cikin gaggawa.
“Kada wani gidan man fetur ya kuskura ya sayar da fiye da lita 50 ga kowace mota a lokaci guda. Daga yanzu kuma, gidajen mai za su sayar da mai ne tsakanin ƙarfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.
“Sayarwa ko yawo da biredi, yanzu zai zama kawai a Hedikwatar kowace Ƙaramar Hukuma: Amma a Gusau, an amince a sayar a yankunan: Hanyar Damba—Zaria; Gada Biyu—Sokoto; Command Guest House a hanyar Ƙaura Namoda; Gusau Garage—Dansadau.”
Haka kuma dokar ta No. 04, 2024, wacce Gwamnan ya sanya wa hannu, ta haramta motoci masu ɗauke da gilashi mai duhu a Zamfara. “Haka kuma an haramta wa masu motoci rufe lambar motocin su a yayin da suke tafiya.
"Wajibi ne duk masu motoci su kasance tare da cikakkun takardun su, sannan su bi dokar kiyaye dokokin hanya ta jihar Zamfara mai lamba No. 2, 2015, ko duk wata doka da ta shafi wannan.”