An tsinci Gawar Jami'in Tsaron Kwaminiti Wac a Katsina
- Katsina City News
- 13 Mar, 2024
- 652
Masa'udu Masa da Barayin Daji suka kashe bayan kwanaki da Kamashi.
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Da Yammacin ranar Laraba 13 ga watan Maris aka Tsinci Gawar Jami'in Tsaron Al'umma na "Katsina Community Watch Corps C-WATCH, Masa'udu Masa a Bayan garin Yasore dake karamar hukumar Batsari jihar Katsina. An Yi Jana'izar sa, kamar yanda Addini ya tanada a garin na Batsari.
Masa'udu Masa jami'in na C-WATCH shi ne na Uku da ya Rasu, bayan tabbacin Mutuwar Mutum biyu a lokacin da Barayin Daji suka yiwa Jami'an Kwanton Bauna a Dajin Yasore dake Batsari ranar Lahadi goma 10 ga wata Maris 2024. Tun daga wannan hari Ba'asake ganin Masa'udu ba sai ranar Laraba da misalin karfe daya 1 na rana da aka tsinci gawar tasa.
Garin Batsari da wasu kananan hukumomi 9 a Yankunan jihar Katsina suna fama da Matsalar tsaro, wanda a kusan kullum sai an kashe ko an kona ko an sace.
Gwamnatin jihar Katsina da jami'an tsaro gwamnatin tarayya suna iya kokarinsu na ganin bayan matsalar, wanda ko a makon da ya gabata Gwamnan jihar Katsina malam Dikko Umar Radda ya Siyo wasu manyan Motocin Yaki da ake kira APC domin Tunkarar yakin gadan-gadan.