Ana Wata Ga Wata:- Cikin Azumin nan Ƴanbindiga sun sake sace mutum 61 a Kaduna
- Katsina City News
- 13 Mar, 2024
- 678
Ƴanbindiga sun sace kimanin mutum 61 a karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna, arewa maso yammacin Najeriya.
Ƴanbindigar sun kai harin ne a garin Buda ranar Litinin da daddare suka buɗa wuta, kamar yadda wasu mazauna yankin suka shaida wa BBC.
Sai dai babu wata sanarwa daga hukumomin jihar da jami'an ƴansanda da ke tabbatar da harin.
Amma mazauna yankin sun ce ƴanbindigar sun yi wa garin ƙawanya ne da misalin karfe 11:30 na dare suka dinga harbi kan mai uwa da wabi"Ba wanda zai iya fadin adadin ƴanbindigar da suka zo suka tattara maza da mata, waɗanda suka kai kusan mutum 61 da suka tafi da su," kamar yadda wani mazauni garin ya shaida wa BBC.
Ya ce akwai ƴan'uwansa mutum shida cikin waɗanda ƴanbindigar suka tafi da su.
"Mun tantance mata 32 da maza 29 ke hannun ƴanbindigar kuma akwai mai jego cikin matan da suka tafi da su wadda ba ta wuce kwana huɗu da haihuwa inda suka tafi da ita suka bar jaririn," in ji shi.
Ya ce ƴanbindigar sun abka garin ne da niyyar tattara mutane da dama amma taimakon jami'an tsaro da suka kawo ɗauki ne ya taƙaita yawan mutanen da suka sace.
"Ƴanbindigar na cikin tattara mutane sai ga jami'an tsaro sojoji na Kajuru suka buɗe wa ma su wuta suka dinga musayar wuta."
"Ba don shigowar jami'an tsaro ba da ba a san yawan mutanen da za su ɗiba ba," in ji shi.
Ya ce an samu tsaikun samun labarin al'amarin sakamakon rashin hanyar sadarwa ta layin salula a yankin.Harin na Kajuru na zuwa ne mako ɗaya bayan ƴanbindiga sun abka garin Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun inda suka yi awon gaba da ɗaliban makarantun firamare da sakandare 287.
Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren ƴanbindiga ma su satar mutane domin kuɗin fansa. Kuma duk da iƙirarin hukumomin tsaro na ƙoƙarin magance matsalar amma kuma sai ƙara ƙamari take musamman a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.
Satar mutane domin neman kuɗin fansa wata sana'a ce da ke ƙara haɓaka - wani al'amari da ke razana ƴan Najeriya.
Ƴansanda da sojoji duka suna ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya - kuma biyan kuɗin fansa, masana na ganin wata babbar hanyar samun kuɗi ce da za ta ci gaba da rura wutar matsalar.
Wasu hukumomi sun hana biyan kudin fansa, kamar a jihar Kaduna.
Gwamnatin Najeriya kuma ta daɗe tana musanta cewa akwai alaƙa tsakanin ƴanbindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa a arewa maso yammaci da kuma Boko Haram a arewa maso gabashi.
Amma yadda ake ci gaba da satar mutane masana na ganin ya nuna akwai alaƙa tsakaninsu.
Ƴan ƙasar da dama sun yi imanin cewa akwai raunin a ɓangaren tsaro da gwamnoni waɗanda ba su da iko a kan tsaro a jihohinsu.