"Mutum Dubu Talatin Zan ciyar A cikin Watan Ramadana" -Abdul'ziz? Mai Turaka
- Katsina City News
- 11 Mar, 2024
- 618
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Tsohon Mashawarci na Musamman ga tsohon Gwamnan jihar Katsina Malam Amin Bello Masari, akan wayar da kan jama'a, Alhaji Abdul'ziz Mai Turaka ya gudanar da wani yunkuri na ciyar da Mutum dubu 30 a cikin watan Ramadana domin saukaka wa Al'umma.
Mai Turaka ya ya bayyana kudirin ne a yammacin ranar Litinin a gidan sa dake daki tara cikin wata ganawa da manema labarai da ya kira.
Alhaji Abdul'aziz yace, ya bayyana haka ne domin wasu da suka fi shi sukuni ko zarafin yin haka suyi fiye da abinda ya bayyana zai yi.
Yace mun daukar wa kam mu alkawarin cewa, duk rana zamu ga mun bawa mutum dubu abinci, dari biyar a lokacin shan ruwa, dari biyar kuma da Asubahin lokacin yin Sahur.
Malam Abdul'aziz ya kuma yi kira da masu hannu da shuni da su daure su yi fiye da abinda yayi, hakan zai sanya al'ummar jihar Katsina da ma Nijeriya du fita ko su rage matsin da suke ciki. A karshe yayi kira da a dafama Gwamnatin jihar Katsina da Addu'a a karkashin jagoranci Malam Dikko Umar Radda musamman akan abinda ya shafi tsaro, yace Dikko Radda dagaske yake, kuma muna masa fatan Nasara da yardar Allah.