YADDA GAGARUMIN TAIMAKON ABINCIN JAHAR KATSINA ZAI GUDANA A DUK FADIN JAHAR.
- Katsina City News
- 09 Mar, 2024
- 410
@ Katsina Times
1, kowane "ward" a duk fadin jahar na za a sayar da gero da masara buhu dari biyu akan naira dubu ashirin. Mutane hudu ake son su hada dubu biyar biyar su sayi buhu daya.
Ana sayar da gero da masara akan naira dubu arba in da biyar a kasuwa.wannan karya farashi zai tilasta hatta na kasuwa ya kare.
2. Kowace "ward" za a dafa abinci ana bayarwa kyauta.domin buda baki, masu dafawa zasu rika yawo "ward zuwa ward" wannan aikin da dafa abinci zai karade duk fadin " ward"na jahar nan baki daya.a wannan tsarin duk Rana mutane dubu Saba in da daya zasu rika buda baki kyauta
3. Za a raba ma mabukata dubu daya a kananan hukumomi talatin da daya shinkafa mai cin kilo 25 da dubu Goma. An tsara yadda aikin zai gudana da wadanda zasu amfana wadanda aka tabbatar da cewa ne lallai mabukata ne sosai musamman masu lalurar wani bangaren kiki.
4.Aikin an Dora shi bisa Kwamitocin Al umma.a matakin jaha da kananan hukumomi da kuma ward zuwa ward.
5. Gwamnatin Katsina zata sanya ido 24/7 duk inda aka ga wani kes na wasa ko ganganci ko Saba kaidar tsarin aikin za a dau matakin gaggawa.