Yadda Dakatacciayar Minista Betta Edu ta Aikawa babban Akawu ta Ƙasa Takarda bukatar sakar mata Zunzurutun Kudi na ma'aikatar Tallafi na "NSIPA" Har fiye da Naira Biliyan Dubu Sittin da Shida...

top-news



Kamfanin jarida na 'Sahara Reporters' ne ya samu takardar da minista Edu ta rattafawa hannu kuma Mai dauke da kwanan wata na 20/12/2023 aka badakalar wannan manyan kudade.

Dr. Betta Edu dai dakatartar Minista che a Ma'aikatar Jinkai da Rage radadin talauchi wache a ranar 2o ga watan Disamban 2023 ta bukachi babbar Akawu takasa Mrs. Oluwatoyin Sakirat Madein data sakar mata da kudin da suka rage a karshen shekara ta 2023 mallakin hukumar nan ta NSIPA dake kalkashin Ma'aikatar ta Beta Edu ta Jinkai da rage fatara da suka haura Naira biliyan sittin da shidda (N66 billion).

Takardar wache keda taken:
‘NEMAN SAKA KUDIN DA BAA KASHEBA MALLAKAR MA'AIKATAR JINKAI SA RAGE FATARA TA KASA DAGA ASUSUN NSIPA NA KARSHEN SHEKARAR 2023'

Takardar ta minista ta nachigaba da bayanin chewa, "Daga shekarar 2020 ya zuwa yau, Ma'aikatar Jinkai da Rage  Fatara tana da achikin kasafin kudinta na shekar 2023 sauran kudin da ta warewa babban ofishi ko hukumar nan ta NSIPA da ke kula da shirye shirye hudu(3) na bawa Yan kasa agaji da tallafi  kuma dake tabbatar da shirinta yakaiwa Yan kasa sako sa lungu don inganta rayuwarsu Wanda hakan nachikin Kudiri na Farfado da Marataba na wannan Gomnati Wanda a turanche ake Kira da 'Renewed Hope Agenda' 

“NSIPA na fuskantan baban kalu bale wajen rabawa Yan kasa kudaden tallafi da aka ware masu kuma ganin yadda shekar 2023  ke bankwana a karshen wannan wata na Disemba nan muna da ragowar kudaden ba bamu kasheba a asusun ajiyar bankunanmu  kamar haka:

1) NSIO/ Special Intervention 0020208461637 (CBN): N65,828,891,947.58

2) NSIO 0020208461077 (CBN): N500,000,000.00

“A wannan dalilin da na zayyana a sama, muna neman sahalewar Babbar Akawu ta kasa da abamu wayannan kudaden don chigaba da sauke nauyin da yarataya akanmu na biyan duka kudaden da muka tsara kashewa bisa la'akari da mun samu aminchewa daga Shugaban Kasa akan zartar da ayyukanmu.”

“A karshe da Allah ina Miki fatan alkhairi,” Minista Edu ta fada. 

Jimillar dai kudaden da Minista Edu ta nema daga Babbar Akawun ta kasa ta sakar mata a karshen shekarar kasafin kudi ta 2023 zasu kai Biliyan Sittin da Shidda da Miliyan Dari Ukku da Ashirin da Takwas da Dubu Dari Takwas da Tasa'in da Daya da Dari Tara da Arba'in da Bakwai da Kobo Hamsin da Takwas N66,328,891,947.58 sune kuma kamar haka:
(N65,828,891,947.58  N500,000,000.00).

A watan Janairu 8, 2024, Shugaba Bola Tinubu yatsaida Betta Edu daga ofishinta na minista nan take akan wata basakalar kudi wanda hakan na nuni da chewa akwai zarge zargen rashin gaskia da yawa akanta.

Shugaba Kasar ya kuma umurchi hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annadi watau EFCC da ta gudanar ba sahihin binchike akan duk wata alakar kudi a ma'aikatar dama duk wasu hukumomi dake kalkashin kulawar ma'aikatar.

Bugu da kari, Shugaba Tinubu ya kuma yi kira ga Edu da tabada hadin kai ga hukumomin binchiken a lokachin da suke gudanar da binchiken nasu.

Tsaida Minista Edu daga mikamin nata dai ya biyo bayan rehoton zargin almundahana na wasu kudaden Jinkai da ta tura a asusun ajiya na daidaikun (individual accounts)na maikatanta Wanda yin hakan sabawa dokane. 

Idan mai karatu bazai mantaba, Sahara Reporters kamin wannan lokachin ta taba kawo maku rehoton yadda Edu ta nemi Babbar Akawu ta Kasa Mrs. Madein da ta tura wasu kudade na jamaa a asusun Mai zaman kanshi da ake kira ' private account' a turanche.

A wanchan lokachin, takardar da 'Sahara Reporters' tasamu ta nuna chewa asusun da aka tura kudaden sune asusun ajiya mallakar Oniyelu Bridget Mojisola, wanda kuma Project Manager ne na wani camfani na wani minista a Najeriya. 

Takardar daga Minista mai lamba: FMHAPA/HQ/OHM/S.208 zuwa ga Babbar Akawu takasa, Mrs Madein mai dauke da kwanan wata 20 ga watan Disemba, 2023, ta roki atura N585 million a wasu asusun ajiya ba bisa ka'ida ba.

Takardar da Minista Dr. Edu ta rattafawa hannu mai taken: ‘Aminchewar sakin kudi don biyan mutane marassa galihu a jihohin Akwa Ibom, Cross River,  Lagos da Ogun’.

Takardar na kunshe da bayani kamar haka, “ Na aminche da biyan kudaden da jimillarsu takai Naira Miliyan Dari Biyar da Tamanin da Biyar da Dubu Dari da Tamanin da Tara da Dari Biyar chif chif (N585,189,500.00). Wannan dan biyan kudin wasu shirye shirye da ayyuka na 'Renewed Hope Grant for Vulnerable Groups.”

Takardar ta kara bayani kamar haka: N219,429,750.00  Giran na 2023 na mutane marassa galihu(Vulnerable Groups) a jahar Akwa Ibom; Sai kuma N73,828,750.00 Giran na 2023 na Mutane marassa galihu (Vulnerable Groups) a jahar Cross River; Sai Kuma  N219,462,250.00 Giran 2023 na mutane marassa galihu (Vulnerable Groups) a jahar Lagos State. Sai kuma N72,468,750.00 Giran 2023 na rukunin mutane marassa galihu (Vulnerable Groups) a jahar Ogun.

Takardar tache duka jimillar kudin N585,189,500.00 zaa turasu ne a asusun ajiya na United Bank For Africa (U.B.A) Mai lamba  2003682151 mallakin Oniyelu Bridget Mojisola.

“Za'a biya wayannan kudin daga asusun ajiya na ofishin 'National Social Investment Programme' dake da asusun ajiya Mai lamba: 0020208461037 zuwa asusun ajiya na Project Accountant kamar yadda aka gani a sama.
 
Kuma dai a ranar ta 6 ga watan Nowamba na 2023 ma'aikatar ta aminche da atura N72,423,250 million zuwa Jahar Bayelsa daga 2023 giran na tsarin mutane marassa galihu da ake kira a turanche  'vulnerable groups programmes'.
 
Kuma adai 3 ga watan Nuwomba 2023 Maaikatar ta tura N81,390,750 million zuwa Jahar Imo kamar dai yadda akayi a Jahar Kogi kwana 7 kamin zaben gomna a jahar.
Kamar yadda takardun suka bayyanna,  Minsta ta Jinkai da rage fatara Dr. Betta Edu ita dakanta ta aminche atura kudin a wannan jihohin guda ukku.
A ranar 31 ga watan Oktoban bara,  Majalisar dokoki ta tarayya ta gayyachi Minista Edu don bata bahasi akan shirin tallafin nai dubu ashirin da biyar N25,000 da zaa bawa magidanta masu karamin karfi a fadin Najeriya su miliyan 15.

A lokachin bayyan korafin al"umma mai muhimmanchi, Majalisar ta bayyana samuwarta akan yadda shirye shiryen ke gudana inda tache ana nuku nuku kuma akwai alamun almundahana.

Yayin zaman, yan majalisun sun bukachi Ministar da tayi gamsan shen bayani abaki kuma tabada a rubuche hanyoyin da maaikatar tata tabi wajen samun bayanen wayanda zasu amfana da kuma yadda zaa raba masu kudaden har suje wajensu ba tare da samun tangarda ba.

NNPC Advert