Jami'an tsaron Al'umma sun yi wa Matar Aure Dukan kawo wuka a Katsina

top-news

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 

Jami'an tsaron Al'umma, da aka fi sani da "Katsina Community Watch Corps" (C-WATCH) a garin Danmusa sun yi ma wata mata Dukan kawo wuka a kan rikicin Aure.

Kamar yanda Matar Zulaiha ta bayyana ma wakilin mu, cewa sun samu hatsaniya da maigidanta da ake kira Amadun Kyauta, a ranar Litinin 4 ga watan Maris, inda ya kai kararta ga jami'an Al'umma (Community Watch Corps) suka zo har gida suka tafi da ita, tace: "Da zuwan mu Ofishin su, suka tambayeni mijina ya kawo kara a wajensu wai naja mashi sharrin sata..!" Ba tare da sun tsaye sunji mi zance ba, suka sanya itacen Bedi tsamgu masu kwari suka taru a kaina sukaita bugu na da zagina suna tsine mun akan cewa, "Dan'uban da ya haife ni ba miji na bane, da yake bani ci da sha, shine zan ce ya satar mun batirin waya".

"Sun buge ni sosai sun ji mun ciwo duk jini ya kwanta mun a jiki, kuma gaban Mijin nawa, sana suka tsare ni daga bisani suka sake ni."

"Jami'an Katsina Community Watch a karamar hukumar Danmusa sun koma shari'ar Aure, bin Bashi, da sauran Abubuwan da da don shi aka dauke su ba, sana kuma suna zaluntar mu, da sunan kakin da ke jikin su". Inji wasu mazauna garin Danmusa da muka zanta da su.

Game da wannan lamari, Mun samu Jin ta bakin Jami'an na C-WATCH a ƙaramar hukumar Danmusa, amma sun bayyana mana cewa "A hukumance an hanasu magana da 'Yan Jarida, don haka ba zasu ce komai ba".

Katsina Times ta samu Hoton Malama Zulaiha da irin raunin da akai mata amma kasantuwar ta na Mace, kuma Matar Aure, sun jimata rauni inda ba zamu iya nunawa ba don kare mutuncin ta.

NNPC Advert