Mataimakin shugaban kasa Shettima ya gana da Buhari a Daura
- Katsina City News
- 02 Mar, 2024
- 510
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a ranar Asabar ya ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a garin Daura na jihar Katsina.
Shettima ya gana da Buhari ne tare da ministan noma, ministan kasafin kudi, Sanata Rochas Okorocha, da wasu manyan baki.
Mataimakin shugaban kasar ya samu tarba daga gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua dake Katsina.
Kakakin Shettima, Stanley Nkwocha ne ya bayyana taron a shafin sa na X.
Ya rubuta: “A yanzu haka mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya isa garin Daura na jihar Katsina.
"A halin yanzu shi bakon tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne.”