Shettima Ya Tabbatar Da Cewa Gwamnatin su Ta Samar da Sabbin Dabarun Yaki Da Rashin Tsaro
- Katsina City News
- 02 Mar, 2024
- 607
Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettina ya bada tabbacin cewa Gwamnatin tarayya zata samar da sabbin dabarun yaki da ‘yan fashi da makami da Garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro a sassan kasar nan.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne bayan wata ganawar sirri da ya yi da Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Gidansa dake Daura a jihar Katsina A Yau Asabar.
Wannan tabbacin yazo ne kwana guda bayan Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya roki Gwamnatin tarayya da ta kara tura jami'an tsaro da kayan aiki Domin tallafa wa jihar a lokutan da take fama da hare-haren ‘yan fashi da makami.
Shettima Yace Gwamnatin tarayya zata tura duk wani abu da kwararrun da ake buƙata domin dawo da tsaro da zaman lafiya a yankunan da suke fama da matsalar Rashin tsaro a jihar Katsina
Ya ce Gwamnatin Tinubu ta kuduri aniyar cika alkawuran da ta ɗauka wa ‘yan Najeriya a yakin neman zabe duk da kalubalen da ake fuskanta na tattalin arziki yayin da ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da marawa Gwamnatin baya da addu’a.
Yayin da mataimakin shugaban ya sauka a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua dake Katsina, ya samu tarba daga Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda da wasu manyan jami’an Gwamnati a jihar.
Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu rakiyar ministan kasafin kudi da tsare-tsare na tattalin arziki Sanata Atiku Bagudu da na noma da samar da abinci Sen Abubakar Kyari da kuma tsohon Gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha sun kuma kai gaisuwar ban girma ga Sarkin Daura. , Alhaji Umar Faruk Umar a fadar sa dake Daura.