Yan bindiga sun kashe mutum 6 a Unguwar Mairabo dake Malumfashi
- Katsina City News
- 27 Feb, 2024
- 600
An yi zana'idar akalla mutum 6 da 'yan bindiga suka kashe a ƙauyen unguwar Mairabo dake Yamma da garin Marabar Ƙanƙara, da ka wuce Unguwar Gambo, karkashin karamar hukumar Malumfashin jihar Katsina.
Kamar yadda majiyar Katsina Daily News ta rawaito, maharan sun fara kai ma al'ummar ƙauyukan hari ne tun wajen karfe hudu na yamma har zuwa karfe 9pm na daran jiya Litinin.
Wani mazaunin yankunan Nabil Yahaya Karfi, ya sheda mana cewa a yanzun haka mutanen kasar Karfi da Yaba, da damansu na ta tserewa daga garuruwan nasu zuwa gudun hijira, inda ya kara da cewa "wasu ma tafiyar kawai suke yi ba su san inda za su ba"
"Ko a jiya ma babur biyar suka shiga unguwar Makera arewacin Karfi inda suka kashe mutum 1 sun kone gidaje aƙalla biyar, da motoci da rumbunan hatsi" Inji Yahaya Karfi.
Sai dai har kawo hada wannan rahoton ba mu ci karo da wata sanarwa da hukumomin tsaro suka fitar ba game da wannan sabon harin na karamar hukumar Malumfashin ba.