An gabatar wa da Gwamna Dauda Lawal cikakkun bayanai kan yadda ayyuka daban-daban ke gudana a Jihar Zamfara.
- Katsina City News
- 26 Feb, 2024
- 363
Gwamnan, wanda ya jagoranci taron Majalisar zartarwar jihar Zamfara a ranar Litinin a zauren majalisar da ke gidan gwamnati a Gusau, ya amshi rahotannin ayyuka daban-daban da gwannatin ke aiwatarwa a duk faɗin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa majalisar zartarwar ta zauna a karo na goma sha shida tun hawan gwamnatin Gwamna Dauda Lawal.
A cewarsa, shugaban majalisar, Gwamna Lawal, ya samu cikakkun rahotanni kan ci gaban da aka samu, da ƙalubalen da aka fuskanta, da kuma lokacin da ake sa ran kammala kowane aiki.
Waɗannan ayyuka da ake gudanarwa sun shafi sassa daban-daban, gami da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da tilasta bin doka.
A yayin jawabin da ya yi wa majalisar, Gwamna Lawal ya jaddada muhimmancin 'aikin ceto Zamfara' na gwamnatinsa, wanda ya ba da fifiko wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana.
“Muna da babban nauyi a gabanmu yayin da muka fara aikin ceto. Burin mu shi ne cetowa, tare da sake gina Zamfara, kasancewar ba mu da wani wurin da za mu kira gida sai nan.
“Na amince da ɗaukar ma’aikata 250 aiki a Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Zamfara (ZAROTA) nan take domin inganta ayyukan gine-ginen da gwamnatina ke gudanarwa a cikin birane.
“Na umurci kwamishinan shari’a da babban lauyan gwamnati da su kafa kotun da za ta kula da laifukan da suka shafi ababen hawa.
“Bugu da ƙari, za mu samar da wurare na manyan motoci guda biyu a Gusau domin daƙile cunkoson ababen hawa da tireloli ke haddasawa.”