Gidauniya Mukaddas Anas ta Horas da Matasa 360 a Karamar hukumar Musawa
- Katsina City News
- 25 Feb, 2024
- 478
Gidauniyar ta Mukaddas Anas Foundation (MAF) a takaice ta gudanar da bada horo ga matasa maza da mata fiye da 360 a karamar hukumar Musa ta jihar Katsina,
An bada horon akan Ilimin sana'o,i da kirkire kirkire domin dogaro da kai.
Taron da ya gudana a Makarantar Sakandaren Al'umma ta Dandattijo, ta samu halartar dimbin Matasa da suka fito daga sassa daban-daban na ƙaramar hukumar.
Kamar yanda daya daga cikin masu gudanarwa na cibiyar Alhaji Aminu Anas ya bayyana cewa, "wannan shiri na bada horo da tallafawa matasa zaici gaba da bullo dabaru daban-daban don kyautata rayuwar Mata da Matasa domin dogaro da kai. Haka zalika yayi kira ga wadanda zasu ci gajiyar shirin da su maida hankali da abinda zasu koya domin amfanin kansu da kansu.
Masa daban-daban a wajen taron sun gudanar da kasida akan muhimmancin Sana'o'in Hannu da kuma amfanin su wajen ci-gaban rayuwar Al'umma.
Wasu da suka samu horon sun nuna farin cikinsu akan abinda suka koya da kuma kira ga sauran al'umma da masu iko da su biyo irin wannan tsarin na gidauniya ta Mukaddas Anas.
Cibiyar ta Mukaddas Anas an kirkireta ne domin gwadawa da koya dubarun Sana'o'i ga matasa Maza da Mata gami da basu jarin dogaro da kawukansu, da kuma basu shedar samun horon.