Danmajalisar Tarayya a karamar hukumar Katsina ya Kaddamar da Aikin Titi a karamar hukumar.
- Katsina City News
- 23 Feb, 2024
- 470
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Danmajalisar Tarayya daga karamar hukumar Katsina Honorabul Sani Aliyu Danlami ya kaddamar da Aikin Titin Kofar Sauri zuwa Babban Titin da ya gewaye Katsina (Ring road).
An kaddamar da fara aikin ne a ranar juma'a 23 ga watan Fabrairu 2024, Unguwar Kofar sauri cikin garin katsina.
Wa wajen Taron Danmajalisar wakilan Honorabul Sani Aliyu Danlami ya bayyana cewa, a yau ya cika Al'kawari da ya dauka a baya na cewa zai gabatar da wasu manyan Ayyuka na Titi guda uku a cikin garin Katsina, yace "Yau na cika Al'kawari kuma ba shi kenan ba akwai wasu a cikin Layout, Abatuwa da sauran mahimman wurare da insha Allah, nan ba da jimawa ba suma zamu kiraku mu kaddamar dasu.
Titin da zai fara daga Kwanar kofar sauri zai bi ta gaban Lambun Danlawan ya fita Kukargesa zuwa Babban Titin Ring road ana sa ran kammala aikin a cikin watanni uku kamar yadda Injiniyan ya tabbatar.
Kimanin watanni biyu da suka gabata ne Danmajalisar Sani Aliyu Danlami da aka fi sani da Mairaba Alheri ya kaddamar da gina Rijiyoyin Burtsate guda 100 da Fitilun Sola, guda 150 a karamar hukumar Katsina.