Ƙungiyar Masu Biredi Ta Nijeriya Ta Nemi Membobinta Su Dakatar Ayyukansu
- Katsina City News
- 20 Feb, 2024
- 474
Daga Zahraddeen Sirajo Abbas
Ƙungiyar masu Biredi da haɗa kayayyakin abinci da fulawa ta Nijeriya, wato AMBCN a taƙaice ta shelanta dakatar da ayyukanta na aƙalla mako ɗaya idan gwamnatin ƙasar ba ta yi wani abu ba na ganin farashin kayayyakin haɗa biredi bai sauka ba.
Ƙungiyar har wala yau ta nemi dukkanin membobinta a faɗin ƙasarnan da su dakatar da ayyukansu nan take har sai sun ji sabon sanarwa daga uwar ƙungiyar.
Wannan shela na ɗauke ne a wata sanarwar cimma matsaya da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Mansur Umar, da Sakataren ƙungiyar Jude Okafor suka sanyawa hannu a makon nan bayan cimma matsaya da majalisar zartarwa ta ƙasa na ƙungiyar suka yi.
Sanarwar ta ce; shugaban ƙungiyar masu Biredi ta Nijeriya, ya ce bayan la'akari da cimma matsaya ta dakatar da gudanar da ayyuka tare da bayar da sanarwar hakan domin samar da kyakkyawan sakamako mai ma'ana, suna mai sanar da abubuwa kamar haka;
"Daga ranar 27 ga watan Fabrairun 2024, za a dakatar da gudanar da ayyuka a ƙasa baki ɗaya har na tsawon mako guda, sai dai idan gwamnati ta iya magance matsalar tsadar fulawa da sikari da sauran kayayyakin haɗa biredi", in ji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa; "Shugaban ƙungiyar na ƙasa ya umurci dukkanin jihohin da har yanzu ba su gabatar da takardun matakinsu ba ga gwamnatin jiharsu da su yi hakan nan da ‘yan kwanaki masu zuwa sannan su aika da kwafin takardar da aka amincewa zuwa dandalin AMBCN na ƙasa.
"Dukkan jihohi su yi taron manema labarai a jihohinsu daban-daban domin shelanta dakatar da ayyukansu bai ɗaya a matakin ƙasa. Dole ne a aiwatar da wannan a ko kafin ranar Laraba 21 ga Fabarairun 2024.
"Dukkan shugabannin jihohi za su halarci taron dakatar da ayyukan na ƙasa a hukumance ta hanyar halartar taron manema labarai na ƙasa a Legas inda masana'antun fulawa suke", in ji sanarwar.
Har wala yau ƙungiyar ta ƙara da cewa; "an ɗora wa tawagar kafafen yaɗa labarai na ƙungiyar na ƙasa alhakin ganin cewa dukkan jihohin ƙasar nan da babban birnin tarayya Abuja sun yi aiki da waɗannan matakan da kuma gaggawar komawa ga Shugaban ƙungiyar na ƙasa da Sakatare".
Ta ƙarƙare da cewa; "Dukkanin jihohi ya kamata nan da nan idan ba su yi ba tukunna to da su yi ƙarin farashin kayayyakin su a kan aƙalla naira 1.50k kan duk giram 1 na kwaɓi. Wannan shi ne abin da zai taimaka mana mu tsaya da ƙafafunmu bisa la'akari da hauhawar farashin kayayyakin haɗa biredi."