Sarkin Katsina Ya goyi bayan Kafa Hukumar Hisbah A jihar Katsina
- Katsina City News
- 20 Feb, 2024
- 598
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A wata muhimmiyar ziyara da Shugaban hukumar Hisbah ta jihar Katsina ya kai fadar mai martaba sarkin Katsina ranar Talata, 20 ga Fabrairu, 2024, Mai Martaba Sarkin Katsina, Dr. Abdulmuminu Kabir Usman, ya bayyana matukar gamsuwa da amincewa dangane da kafa hukumar Hisbah a jihar.
A cikin ziyarar da Shugaban na Hisbah ya kai a masarautar Katsina da Ofishin hukumar tsaro ta farin kaya (Civil Defence) Sarkin na Katsina ya bayyana gamsuwa da farin cikinsa na samar da Wannan hukuma inda yace shi aka taimaka da aka samar da ita.
Kwamanda Janar Aminu Usman, PhD, shugaban sabuwar hukumar ta Hisbah, ya bayyana manufar hukumar, inda ya bayyana yadda Gwamna Dr. Dikko Umar Radda ya kirkiro ta domin magance kalubalen da al’umma ke fuskanta. Yunkurin da gwamnan ya yi na samar da hukumar shi ne don yakar laifuka da gurbacewar tarbiyya, tare da mayar da hankali wajen shirya tarurruka da bayar da shawarwari kan aure domin dakile karuwar zinace-zinace.
Da yake neman shawarwari da tallafi da hadin kai daga shugabanni, malamai da iyaye, Dokta Aminu Usman ya jaddada hada kan hukumar, tare da hada kan mabiya Addinin Musulunci da kungiyoyi daban-daban domin ci gaban jihar Katsina.
Mai martaba Sarkin Katsina Dr. Abdulmuminu Kabir Usman CFR, ya bayyana jin dadinsa da kafa hukumar ta Hisbah, inda ya bada tabbacin samun nasarar ta idan an kaucewa son zuciya da siyasa. Mai martaba ya ba da shawarwari ga hukumar ta gudanar da aikinta yadda ya kamata, ya kuma kara da niyyar ba da duk wani taimako da ya dace.
Jamilu A Indabawa, Kwamandan tsaron farin kaya (Civil Defence) na jihar Katsina, ya yabawa Gwamna Mal. Dikko Umar Radda bisa kafa hukumar ya kuma yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga kokarin hukumar Hisbah na kawo gyara ga al’ummar jihar Katsina. Indabawa ya yaba musamman jarumtar kwamandan hukumar Dr. Aminu Usman (Abu Ammar).
Tawagar hukumar da ta hada da Alh. Abdulaziz Abba Umar, daraktan gudanarwa, daraktan kudi, manyan jami’an hukumar Hisbah, da kuma wakilan kungiyoyin dariƙu a jihar Katsina, domin cimma hadafin farfado da tarbiyya a jihar.