Aikin Wutar Lambar Rimi a jihar Katsina: Dan majalisa ya gabatar da Korafi a zauren Majalisa.
- Katsina City News
- 19 Feb, 2024
- 627
Arc. Murtala Usman Banye, Dan Majalisar Tarayya daga kananan hukumomin Batagarawa, Rimi da Charanci, ya gabatar da korafi a zauren Majalisar Wakilan Nijeriya kan ko in kula da aka yi da Aikin wutar Lambar Rimi ta jihar Katsina fiye da shekaru goma ba tare da an kammla Aikin ba.
Da yake gabatar da korafin Honorabul Banye, yace Aiki ne da Gwamnatin Tarayya ta fara tun lokacin tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa Yar'adua, wanda aikin yayi ta tafiyar hawainiya a karshe aka watsar.
Hon. Ya bayyana Aikin Wutar mai karfin MegaWat 10 da cewa Babbar gazawa ce ace an kwashe tsawon wannan shekaru ba tare da Aikin ya kammala ba.
Usman Banye ya bayyana gagarumin cigaba da samar da wutar mai Aiki da Iska zai samar a jihar Katsina idan har aikin ya kammala.
Karshe yayi kira ga Zauren Majalisar da duba yiyuwar maido da Aikin domin cigaban jihar Katsina, yankunan Arewa maso Yamma da kasa baki daya, ta fuskanci Tattalin Arziki, bunkasa masana'antu da samar da Ayyukan yi.