Gamayyar Kungiyoyin fararen Hula a Katsina Sun Bukaci sa Hankali A Cikin Matsalolin Najeriya a maimakon Zanga-zanga
- Katsina City News
- 18 Feb, 2024
- 720
Gamayyar Kungiyoyin fararen Hula a Katsina Sun Bukaci sa Hankali A Cikin Matsalolin Najeriya a maimakon Zanga-zanga
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A cikin wata Tattaunawa da kungiyar hadin kan Katsina Groups for National Unity and Integration, kungiyar masu zaman kansu a jihar Katsina suka yi, kungiyar ta bayyana kudurin ta na tabbatar da adalci, zaman lafiya, dimokuradiyya, da kyakkyawan shugabanci.
Kungiyar ta jaddada matsayinta na masu goyon bayan tattaunawa, don samar da hadin kai da fahimtar juna.
A yayin da take tinkarar kalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu, kungiyar ta amince da kokarin gwamnati wajen magance matsalolin da suka hada da tsadar rayuwa da rashin tsaro.
Gamayyar kungiyoyin sun amincewa da matakan da Gwamnatin Tarayya ta dauka da suka hada da biyan N35,000 ga ma’aikata, kaddamar da kwamitin mafi karancin albashi na kasa, da kafa cibiyoyin canza iskar gas, kungiyar ta yaba da matakan da aka dauka don magance wadannan matsalolin.
Kungiyar ta kuma amince da yunkurin gwamnatin na yaki da cin hanci da rashawa, inda ta bada misali da wasu ayyuka na musamman na cin hanci da rashawa, da suka hada da dakatar da minista da kuma binciken jami'ai irinsu Godwin Emiefele. Musamman ma, gamayyar kungiyoyin sun yi tsokaci kan hada hannu da gwamnonin jihohi domin magance tashin farashin kayayyaki da rashin tsaro.
Da take bayyana ra'ayi kan zanga-zangar da N.L.C ta shirya yi a fadin kasar, gamayyar kungiyoyin sun nuna cewa Zanga-zanga ba zata taba zama mafita ba, illa tattaunawa a tsakanin kungiyoyin da gwamnati.
A yayin da kungiyar ta amince da kudirin gwamnati na shigar da kungiyoyin kwadagon, kungiyar ta ba da shawarar hana zanga-zangar kan tituna, tare da jaddada bukatar ci gaba da tattaunawa har sai an biya bukatun.
Dangane da zanga-zangar da aka yi a baya, ciki har da #ENDSARS, gamayyar ta yi gargadi kan ayyukan da za su iya gurgunta zaman lafiya, tare da yin kira ga kungiyoyin kwadago da su guji matakan da za su cutar da zaman lafiyar da ake ciki.
Gamayyar kungiyoyin sun yi Allah wadai da masu cin gajiyar wahalhalun da 'yan Najeriya ke ciki domin cimma wata manufa ta siyasa. Bugu da kari, sun yi kira ga kananan hukumomi, masu rike da mukaman siyasa, masu zaman kansu, da masu hannu da shuni da su bayar da tasu gudummawar wajen rage wahalhalun da talakawa ke fuskanta.
A tattauna da gamayyar kungiyoyin suka kira a babban dakin taro na Ofishin Kungiyar ma'aikatan lafiya ta jihar Katsina, sunji ra'ayoyin kungiyoyi da daidai kun al'umma akan kaucewa zanga-zanga don gudun tayar da fitina.
Kungiyoyin sun amince da samun maslaha ta hanyar tattaunawa da kuma kira ga gwamnatoci jiha da kananan hukumomi gami da Majalisar Dokoki da ta Tarayya da su duba lamarin Talakawa a cikin gaggawa.
Gamayyar kungiyoyin sun yaba da yunkurin gwamnatin jihar Katsina na daukar matakai akan tsaro, da hanyoyin da tabi don kawo sauki ga hauhawar farashin abinci. Saidai Kungiyoyin sun yi kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta sake duba Tallafin ma'aikata na naira dubu 15 da take bayarwa.
Babban mai bawa gwamnan jihar Katsina shawara akan wayar da kan jama'a Alhaji Sabo Musa Hassan yayi tsokaci akan halin da aka shiga inda ya bayyana cewa, Matsala tana ga masu hannu da shuni da su kansu talakawa, a inda ya maida lamarin da cewa duka sai anji tsoron Allah an kyautatawa juna.