ME YASA JAHAR ZAMFARA TA KAFA ASKARAWAN ZAMFARA?
- Katsina City News
- 17 Feb, 2024
- 581
@ Katsina Times da Jaridar Taskar labarai
Wannan wata tattaunawa ce jaridar Daily Trust ta yi da Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, inda a ciki ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatin sa ta kafa rundunar tsaro ta jihar da aka yi wa laƙabi da ASKARAWAN ZAMFARA (CPG) domin su taimaka wa jami’an tsaro a yaƙin da ake yi da ayyukan ‘yan ta’adda da sauran masu laifukka a sassan jihar.
Mun fassaro wannan tattaunawa ce saboda irin muhimman bayanan da Gwamnan ya yi na ciyar da jihar Zamfara da Zafarawa gaba. Ga dai yadda hirar ta kasance.
Tambaya: Mene ne dalilinku na kafa wannan rundunar tsaron da aka yi wa laƙabi da ASKARAWAN ZAMFARA?
Gwamna Lawal: Kamar yadda aka sani ne, Jihar Zamafra na fuskantar matsaloli da dama, daga cikin su kuma akwai matsalar tsaro, an yi shekaru a na yaƙi da mastalar, ta ƙi ci ta ƙi cinyewa; saboda haka duk wata gwamnati da ta damu da al’amuran mutanen ta, dole ta muhimmantar da lamarin tsaro. Wannan shi ne babban dalilin da ya sa muka shirya samar da wannan rundunar.
Alhamdu lillahi sun samu horo na tsawon wata biyu da rabi, an kuma ƙaddamar da su don su fuskanci yaƙi da ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, ɓarayin shanu da dukkan nau’o’in ta’addanci da rashin tsaro a duk faɗin Jihar.
Wannan gwamnatin ta zuba jari mai yawa don kawo ƙarshen ayyukan ‘yan ta’adda da sauran ayyukan ɓata-gari a jihar. Babu wata gwamnati mai mutunci da za ta yi sako-sako da harkokin tsaro.
A halin yanzu mun ƙaddamar da dakaru 2,645 a zango na farko, muna sa ran ɗaukar dakaru fiye da 5,000, za a ci gaba da ɗaukar ne daki-daki. Za mu auna su mu ga yadda suke gudanar da aikin su, da kuma irin ƙalubalen da suke fuskanta, daga nan za mu yanke shawarar ɗaukar ƙarin dakarun in akwai buƙatar haka.
Kamar yadda na ce, samar da tsaro na da muhimmanci don kuwa babu wani abin da za a iya yi a jiha, da ma ƙasa baki ɗaya in har babu cikakken tsaro.
Mun samar da dukkan abin da ake buƙata don samun nasarar dakarun na CPG, tun daga lokacin da aka ɗauke su aiki da horas da su, don mun tabbatar da aikin su yana tafiya yadda ya kamata kuma cikin sauki.
Gwamnati ta samar musu da kayan aiki na zamani, tun daga motocin sintiri, kayan sadarwa, mashina don su samu sauƙin gudanar da aikin su, mun kuma ba su alawus-alawus ɗin su tun daga lokacin da aka fara horas da su har zuwa yanzu, za kuma mu ci gaba da ba su kuɗaɗen su na wata-wata.
Muna kuma shirin sanya su a cikin tsarin ishora, musamman ganin irin haɗarin da ke tattare da aikisu. Muna haka ne don ƙarfafa su wajen gudanar da aikinsu.
Tambaya: Yaƙi da mastalar tsaro na buƙatar dabaru da dam. Wani mataki za ku ɗauka bayan ƙaddamar da rundunar Askarawan Zamfara?
Gwamna Lawal: Lallai haka abin yake, yaƙi da matsalar tsaro na buƙatar dabaru da dama, dole ka fahimci irin matsalar da kake fuskanta. Dole ka fahimci wurin da ke gudanar da yaƙin, ya kuma kamata ka fahimci dalilin da ya samar da irin ta’addacin da kake fuskanta da sauransu.
Waɗannan dakarun za su taimaka wa ayyukan jami’an tsaron mu ne, irinsu ‘yan sanda, sojoji, DSS da Sibil defence wajen yaƙi da ‘yan ta’adda. Muna fatan haɗa dabaru ne masu yawa, amma hanƙoron mu gaba ɗaya shi ne yaƙi da ‘yan ta’adda a duk sassan jihar.
A kan haka ne na ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangarori biyu masu muhimmanci, sashin ilimi da lafiya. Kamar yadda ka sani in har kana son samun nasara a yaƙi da ta’addanci, to dole ka ɗaga darajar rayuwar al’umma, saboda hakan zai taimaka wajen rage ayyukan masu aikata laifi a cikin al’umma.
Ina mai tabbatar muka da cewa, a cikin wata shida mai zuwa, da ikon Allah za a ga canje-canje masu muhimmanci a Zamfara, musamman a ɓangarori uku; tsaro, lafiya da ilimi. Byan wadanna ɓangarori uku, ana ci gaba da gine-ginen hanyoyi a babban birnin jihar, Gusau, ayyukan sun yi nisa sosai. An fara aikin ne nan take bayan mun kama aiki, kuma duk da matsalolin shari’a da muka fuskanta ba mu dakatar da aikin ba. Alhamdu llilah a halin yanzu babu wata shari’a a wuyan mu, saboda haka al’ummar Jihar Zamfara su saurari ayyukan ci gaba daga wannan gwamnatin, domin sun zaɓe mu ne don mu yi musu aiki, kuma za mu yi musu aiki, da yardar Allah ba za mu ba su kunya ba.
Tambaya: Rahin Haɗin kai da aiki tare shi ne babbar matsalar da ke fuskanta rundunonin tsaron mu. Ta yaya za ka tabbatar da haɗin kai a tsakanin dakarun Askarawan Zamfara da kuma jami’an staron?
Gwamna Lawal: Za mu tabbatar da cikakkiyar dangantaka a tsakanin su. A halin yanzu ma akwai tattunawa ta musamman a tsakanin dakarun Askarawan Zamra da sauran ɓangarorin runudunar tsaron mu. Za mu ci gaba da jawo su kusa. Inda kuma muka samu bambanci ko rashin fahimta a tsakanin su, za mu tattaunawa don mu ci gaba. Ina da tabbacin ba za mu samu matsala da jami’an tsaron mu ba.
Kamar yadda na faɗa, dukkan rundunonin tsaron mu sun bayar da gudummawa wajen kafa dakarun CPG, tun daga ɗaukar dakarun da kuma yadda aka horas da su. Ina da tabbacin dakarun CPG ba za su samu mastala da rundunonin tsaron gwamnatin tarayya ba.
Tambaya: Yana da sauƙi a kafa irin wannan rundunar, amma babbar matsalar it ce tabbatar da ci gaban ta. Wane tabbaci za ka ba al’ummar jihar Zamfara na cewa, dakarun CPG sun zo ke nan?
Gwamna Lawal: To, da farko dai muna da cikakken ƙudurin tabbatar da ganin wannan shirin ya samu nasara, kuma abin da ake buƙata ke nan. A kan haka, ina mai tabbatar maka cewa, za mu tabbatar da ɗorewa tare da wanzuwar dakarun CPG.
Tsaro abu ne mai matuƙar muhimmanci gare mu, ba za mu yi wasa da shi ba, da yardar Allah za mu samu cimma burin mu na kafa rundunar da kuma samun nasara.
Sannan kuma muna da dokar da ta kafa dakarun CPG. Tun da farko sai da muka miƙa lamarin ga Majalisar Dokokin jihar, inda suka zartar da dokar da ta kafa dakarun CPG. Haka kuma a yayin ɗaukar jami’an, mun shigar da Sarakunan gargajiya, tun daga masu Unguwanni, Dagatai, Hakimai da Sarakunan yanka. Mun kuma yi aiki tare da dukkan bangarorin jami’an tsaronmu. Mun yi aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki a ƙoƙarin kafa rundunar Askarawan Zamfara, mu na kuma da tabbacin za su ji daɗin aiki tare.
Tambaya: Dukkan gwamnonin jihohin Arewa sun halarci wannan taron ƙaddamarwa. Me ya mayar da bikin ya zama na musamman?
Halartar su wani babban lamari ne, za ka iya ganin Gwamnonin Kebbi, Sokkwato, Jigawa, Kano, Katsina yayin da mataimakiyar Gwamnan jihar Kaduna ta wakilici jihar, wannan yana nuna yadda shugabanin suka muhimmantar da lamarin tsaro.
Mun yi taruka da dama a tsakanin m, inda muka tattauna matsalar tsaron da ke fuskantar Arewacin Nijeriya, musamman yankin Arewa maso Yamma, wannan kuma yana faruwa ne ba tare da bambancin siyasa ba, lokacin harkokin siyasa ya wuce, yanzu lokaci ne na mulkin al’umma, mun kuma damu da halin da al’ummar mu ke ciki, mun damu da halin da Arewacin Nijeriya ke ciki. A matsayin mu na shugabanin dole mu yi wani abu da gaggawa don magance matsalar da al’ummar mu ke ciki. Wannan shi ne dadlilin da ya sa kaga wannan goyon bayan daga dukkan gwamnonin yankin.
Tambaya: Wani sako ka ke da shi ga dakarun Askarawan Zamfara (CPG) da kuma al’ummar Jihar Zamfara gaba daya?
Gwamna Lawal: Ina kira gare su da su tsayu wajen gudanar da ayyukan su. Sun yi rantsuwar gudanar da ayyukan su ba tare da tsoro ko son kai ba, sun kuma yi rantsuwar kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Zamfara, na kuma yi imani da bayanan da suka yi. Na san za su yi abin da ya kamata, musamman ganin sun rantse ne da Alƙur’ani mai girma, don sun san muhimmacin yin haka.
Ina kuma neman ci gaba da goyon baya daga al’ummar jihar Zamfara ga waɗanna jami’an tsaron na mu, saboda samar da tsaro al’amari ne da ya shafi kowa da kowa. Ina kuma roƙon su ba dakarun CPG cikakken goyon baya, a kuma ci gaba da addu’ar Allah ya ba mu nasarar cimma burin mu. In muka yi addu’a, tabbas Allah zai amsa mana.