"Duk wanda Aka Fasa Sito Aka Saida Masa Abinci Ya Siya, Haram Yaci." Sheikh Yaqub Yahaya Katsina
- Katsina City News
- 16 Feb, 2024
- 768
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Malamin Addinin Musulunci a Katsina Sheikh Yaqub Yahaya, ya bayyana haka a wajen karatun da yake gabatarwa duk ranar juma'a a muhallin karatun dake Unguwar Daki tara a cikin garin Katsina.
Shehin Malamin yaja hankalin Al'umma akan cewa, kuskure ne Gwamnati ta fasa Sito na 'yan kasuwa ta karyas don ta saidawa jama'a, yace "Duk wanda ya saya ya aikata haramun". Saboda ya sayi kayan da aka kwata (Gasabu).
Yace idan har gwamnati da gaske take to ba 'yan kasuwa zata farwa ba da suka je suka nemo kayansu suka aje don kasuwanci, yace shekara nawa 'yan kasuwa na aje abincin su, babu wanda ya taba cewa yana cikin yunwa ko kakanikayi! Ba a taba samun wannan yanayin ba saida aka janye Tallafin mai, ya ce! Ashe kenan Ita Gwamnatin ita ta haddasa halin da ake ciki, shine take so ta juya akan 'yan kasuwa, wannan kuskure ne. Inji shehi.
Yace idan har Adalci gwamnati ta nufa, yakamata ne ta nemi 'Yan Kasuwa ta zauna dasu, ta nemi sauki, sana ta tallafa masu.
Gwamnati ce ta cire tallafin mai, shine asalin duk matsalar da ke faruwa, ya kamata ta maido shi, sai a samu sauki ba ta haddasa matsala sana ta juya ga 'yan kasuwa tace sune matsala ba. Idan ta aikata haka sunan sa kuskure.
"A maida Tallafin Mai, a Karya Dala, idan akai haka mutane zasu samu saukin rayuwa" ya bayyana.
Zamu kawo maku Cikakken Bidiyo a shafin mu na Katsina City News, Sheikh yayi magana akan tsarin Firaminista da ake ta cecekuce akai da kuma halin da kasar ta shiga da Mafita.