"An rufe mana gidan Mai ne don farashin mu yayi ƙasa ga na saura" Ayfir Petroleum
- Katsina City News
- 16 Feb, 2024
- 2904
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Kamfanin na Ayfir da ke samar da Man Fetur a jihar Katsina ya koka akan yanda ake masa bita da kulli daga wasu masu fada a ji da kuma hukumar DPR reshen jihar Katsina.
Da muke zantawa da Kakakin Kamfanin na Ayfir ya zargi Hukumar DPR da kulle masu gidajen mai don sun karya farashin fiye da yanda aka saba saidawa game gari.
Yace "Mai gidanmu yana da dabi'ar saukakawa yanda kowa ke saida mansa, shi yasama ma a lokacin da aka kara kudin mai na cire tallafi inda man yayi tashin gwabron zabi zuwa dari biyar da wani abu, mu bamu kara ba muka cigaba da saida shi a tsohon farashin har sai da tsohuwar dauka ya kara muka dauko sabo." Inji shi.
Ya bayyana cewa "to a yanzu ma haka yanda muke saida man fetur mun rage sosai a lita sabanin saura, hakan yasa wasu suka sanya mana karan tsana, a karshe hukumar da ke kula da gidajen man ta jihar Katsina ta rufe mana gidajen mai gaba daya ba tare da bayyana mana laifin mu ba." Inji shi.
Yace ko da yake bayan fiye da mako guda gidajen man na rufe amma sun bude daga bisani, yace amma idan har akan rage farashin ne ba zasu daina ba don Al'umma su samu sauki.
Game da wannan zarge-zarge da Kamfanin na Ayfir yayi mun tuntubi Mai magana da yawun hukumar ta DPR akan Lambar da muka samu, bata shiga ba mun tura sako na karta kwana shima babu amsa. ya zuwa yanzu dai jami'an gudanarwa na kamfanin na Ayfir sun tabbatar ma Katsina Times cewa an bude masu dikkanin gidajen man nasu.