Hukumar Hizba a jihar Katsina ta cigaba da ziyarar malaman Addinin Musulunci don kyautata Alaƙa
- Katsina City News
- 12 Feb, 2024
- 743
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Sabuwar hukumar ta Hizbah wadda Gwamna Malam Dikko Umar Radda ya Kafa, don kyautata Ɗa'a da Tarbiyyar Matasa, tare da warware rikicin Aure a jihar Katsina ta cigaba da rangadin ta na samun fahimtar juna a tsakanin malaman Addinin Musulunci mabanbanta fahimta a jihar Katsina.
Babban Kwamandan na jihar Katsina Dakta Aminu Usman ne yake jagorantar rangadin a fadin garin Katsina, a na saran hukumar ta Addinin Musulunci da aka samar don umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna zata fadada ziyarar a dukkanin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina don ganawa da Malaman Addini da kuma bangarorin jami'an tsaro da masu rike da sarautun gargajiya.
Sakon da Dakta Aminu Usman yake bayyanawa ga dukkanin malaman Addinin da tawagarsa ta samu ziyarta shine, "Munzo neman Shawara Addu'a da kuma Goyon bayan ku, bisa wannan jaririyar hukuma da gwamnatin jihar Katsina ta kafa don yaki da munanan Dabi'u."
A cikin fahimtar juna da farin ciki, malaman Addinin daga Kungiyoyi daban-daban suke tarbar Dakta Aminu da kuma bashi shawar, gami da goyon bayansu dari bisa dari. Sannan suna kira ga Kwamandan na Hizbah da tawagar sa, akan Jin tsoron Allah, Adalci da Hakuri.
Ziyarar ta ranar Litinin ta fara daga gidan Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Husamatu Abbas Gambarawa, da Sheikh Abdullahi Maisaje, sai shugaban Kungiyar Agaji ta jihar Katsina na Jama'atu Nasrul'islam Alhaji Bilya Sanda da gidan Dattijon Sunnah da ya gina duk wasu manyan masallatan Ahalussunah a garin Katsina Alhaji Abu Modibbo, sai gidan Imam Abbate dake Unguwar Alkali Katsina, da Zawiyyar Khalifa Sheikh Hamisu Danfili, sai kuma Kungiyar Rasulul'a'azam a karkashin jagorancin shugaban kungiyar Sheikh Yakubu Muntari Filin Folo.
Tawagar ta Hizbah ta samu rakiyar jami'in gudanarwa na hukumar da shugaban sashin kudi da Kwamandan Operation da sauran bangarori daban-daban masu dafa masa a cikin tafiyar.