ƳAN BINDIGA SUN KAI MUMMUNAN HARI A KAN HANYAR BATSARI ZUWA JIBIA.

top-news

Misbahu Ahmad  @ Katsina Times 

Ƴan bindiga masu satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, sun kai mummunan hari a kan hanyar Batsari zuwa Jibia. 

A ranar lahadi 11-02-2024 da misalin 06:00pm na yamma ƴan bindiga suka tare motocin ƴan kasuwa da suka dawo daga kasuwar  Jibia zuwa Batsari, inda suka buɗe ma motoci biyu wuta suka kashe mutane takwas (8) sannan suka ƙone motocin.

A yau litanin 12-02-2024 aka kawo gawarwakin bayin Allahn da ƴan bindigar suka kashe a babbar asibitin Batsari ta jihar Katsina. Wanda tuni ƴan'uwan su, suka ɗauke su domin yi masu sutura kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Hareharen ƴan bindiga akan hanyar Batsari zuwa Jibia ba baƙon al'amari ba ne, domin ko a kwanakin baya saida suka tarbe hanyar har suka kaahe mutane, kuma idan ba'a manta ba, sai da gwamnatin jihar Katsina ta taɓa kulle hanyar saboda matsalar tsaro.
Katsina Times 

@ www.katsinatimes.com 
Jaridar Taskar labarai 
@ www.taskarlabarai.com 
07043777779 08057777762

NNPC Advert