Darajar naira na ci gaba da faɗuwa duk da matakin NNPC
- Katsina City News
- 31 Aug, 2023
- 838
BBC Hausa
A na ci gaba da nuna fargaba game da matakin Kamfanin Haƙar Mai na Najeriya, NNPC Limited, na nemo rancen dala biliyan 3 daga Bankin Afirka domin taimakawa wajen farfaɗo da kasuwar musayar kuɗaɗen waje da ke ci gaba da durƙushewa.
Ana dai yi wa wannan matakin kallon mayar da hannun agogo baya kasancewar samun ƙaruwar faɗuwar darajar naira da ake samu da kuma tashin farashin dala a kasuwa.
Wani bincike da Jaridar Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa Kuɗaɗen ajiyar Najeriya na ƙetare na ci gaba da raguwa kashi 0.2 zuwa dala biliyan 33.68, hakan ya faru bayan da Babban Bankin Najeriya, CBN, ya fitar da sanarwar matakin a ranar 16 ga watan Agusta.
A baya dai an ɗauka cewa matakin nemo rancen dala biliyan 3 zai taka rawar a za gani wajen farfaɗo da darajar naira, da kuma saukar farashin dala a kasuwannin musayar kuɗi, wanda ta hakan zai taimaka wajen sauƙaƙa farashin abubuwa a ƙasa.
Daga cikin abubuwan da ke ƙara karya farashin naira har da tsananin buƙatar dala da jama'a ke yi, inda yanzu haka a kasuwar bayan fage a kan sayi dala ɗaya kan naira 920 zuwa 925.