"Kaso Hamsin na Masu Sana'ar Biredi a Najeriya sun durƙushe saboda tsadar Filawa da sukari" -Inji Shugaban Ƙungiyar ta Ƙasa

top-news

Muhammad Ali Hafizy, Katsina Times 

"Muna Rokon Gwamnati Ta Tallafa ma Masu Biredi, kuma Ta Sa Tallafi A Cikin Harkar Alkama Da Sukari"

A cikin wata tattaunawa da jaridar Katsina Times tayi da shugaban kungiyar masu Biredi ta kasa Alhaji Mansur Sani Umar mamallakin gidan Biredin " Mansi Modern Bakery" ya bayyana yadda cire tallafin man ya safi sana'ar su.

A cikin bayanin shi yake cewa "Halin da muke ciki yanzu kaso  Hamsin na gidanjen masu Biredi a kasar nan sun dakatar saboda yanayin da ake ciki" 

Sannan yayi kira ga masu Filawa da Suga da cewa "Su dubi Allah su dubi al'ummar Kasa su tausaya su daina yawan kare-karen nan" sannan ya yi kira ga masu sayen Biredi akan cewa "Su kara hakuri su taya su da Addu'a sun san halin da ake ciki ba dagsu bane babu wani Abu na Biredi wanda bai kara kudi ba.

Daga karshe ya yi kira ga gwamnati da su tallafa ma masu Biredi, sannan su sa tallafi a cikin Alkama da Suga  domin a dawo da komi ya daidai ta.

Akwai cikakkiyar firar a cikin Faifan bidiyo da zamu Kawo maku a shafukan mu na Katsin Times

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *