Cikin wadanda akai garkuwa da su a Kankara hadda Jarirai ...Sun kashe Matashi saura sati ɗaya bikinsa.
- Katsina City News
- 05 Feb, 2024
- 799
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Adadin yawan mutanen da aka dauka ranar Lahadi a garin Katsalle dake karamar hukumar Ƙanƙara ya kai goma sha hudu ciki hadda Jarirai.
Ga Jerin sunaye da gidan da barayin suka farmaka:
Iyalan Abubakar (Dan kasuwa)
1- Uwargidan sa Hadiza
2- Amaryar sa Suwaiba
'Ya'yansa:
3- Abdullahi Abubakar
4- Amina Abubakar
5- Rukayya Abubakar
6- Maryam Abubakar
7- Hafsat Abubakar
8- Halima Abubakar da Jaririyar ta ta goye
Gidan Jari:
1- Uwani Jari
2- Umma Jari
3- Umma Jari
4- Nazifi Jari
Gidan Tijjani
1- Shamsiya Tijjani
Gidan Baban Yara:
1- Hadiza Baban yara
Wannan shine ya bada adadin Mutum goma sha hudu. (14)
Barayin sun kwashi wadannan mutanen ne bayan da suka shiga garin da Magaribar ranar Lahadi 4 ga watan Fabrairu bayan sun kashe Mustafa Ibrahim da ake shirin bikinsa a sati mai zuwa, gami da balle shagonsa da kwasar duk kayan da ke cikin shagon, suka ƙone wani Sito na ajiyar kaya tare da Jikkata Rabi'u Ibrahim da ƙona masa gida gaba daya.
Katsina Times: www.katsinatimes.com
07043777779, 08036342932