ZABEN 2024: KARAMAR HUKUMAR KAITA A MULKIN INJINIYA BELLO LAWAL 'YANDAKI
- Katsina City News
- 02 Feb, 2024
- 989
Sharhin jaridun Katsina Times da Taskar Labarai
@ www.katsinatimes.com
@ www.taskarlabarai.com
Kwanakin baya Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya bayyana wa gidan rediyon BBC a shirin a Fada A Cika cewa, idan wa'adin shugabannin kananan hukumomi ya yi ba zai nada kantomomi ba, sabon zabe gwamnatinsa za ta gudanar. "Gwamnatinmu ba za ta nada kantomomi ba, zabe za ta yi."
Wannan magana ta faranta wa al'ummar Katsina rai, wanda masu jefa kuri'a suka dauki shewa da murna.
A kan haka jaridun Katsina Times suka dauki kudurin nazarin ayyuka da halayen shugabannin kananan hukumomin jihar domin ya zama karatu da yin bita ga al'umma da haskaka fitilar wa za su zaba in an zo laluben wanda za a bai wa jagorancin karamar hukumarsu.
Mun fara daga karamar hukumar Kaita. Sannan za mu ci gaba a hankali daki-daki.
Bayan kammala tattara duk bayananmu, mun yi kokarin jin ta bakin shugaban karamar hukumar Kaita, Injiniya Bello Lawal 'Yandaki, amma hakarmu ba ta cimma ruwa ba.
Wakilanmu sun yi zirga-zirga zuwa hedkwatar karamar hukumar Kaita har sau shida, amma ba ya a ofis, ba kuma wanda ya shirya ya yi magana a madadinsa.
Mun aika masa wasika wadda aka amsa aka sanya hannu, amma babu amsa. Mun koma don jin ko ya bar amsa, amma babu bayani.
Mun aika masa sakon wayar hannu ta lambobinsa da muka samu, duk babu amsa.
Ga kadan daga cikin abin da muka samo maku. Idan bayan rubutun nan ya ba da amsa, za mu kawo maku.
INA TANKUNAN RUWA? WA AKA SAYAR WA?
Binciken da muka gudanar a Kaita abin bakin cikin da muka samu shi ne ana ciccire wasu tankunan ruwa da aka yi don saukaka wa mutanen yankin halin kunci da suke ciki na karancin ruwan sha.
Yankuna da yawa a karamar hukumar Kaita suna cikin halin kunci na ruwan sha, a kan haka ne hukumomin gwamnatin jiha irin su RUWASSA da wasu zabbabbun yankin irin su, Alhaji Musa Nuhu Gafia, Alhaji Salisu Salisco, Alhaji Inusa Dankama, Alhaji Ibrahim Dankaba suka bullo da wani shiri na yin rijiyar burtsatse a hada shi da tankuna don tara ruwa da kuma raba shi ga sauran al'umma.
Wannan aikin ya taimaki mutanen yankin sosai, kuma sun rika amfana da shirin. Wasu tankunan sun dan lalace, wanda suka nemi karamar hukuma ta gyara don ci gaba da aikin su.
Jaridun Katsina Times sun yi magana da wasu da sune suka yi aikin wadannan tankunan na ruwa a fadin yakin Kaita. Kamar 'yan majalisun Tarayya da Sanatoci wadanda aiki suka samo daga gwamnatin Tarayya don a yi wadannan tankunan ruwa da rijiyar burtsatse ga al'umma.
A kiyasin da muka yi an kashe sama da Naira miliyan 300 wajen wannan gagarumin aiki da aka kiyasta in ana kula da shi zai a iya kai shekaru 50 ana cin gajiyar sa.
Zuwan Injiniya 'Yandaki a matsayin shugaban karamar hukumar abin farko da ya fara shi ne sai ya ba da gwanjon tankunan. Haka aka zo aka cire su mutane na nuna fushi da zanga-zanga, wasu wuraren sai da aka hada da 'yan sanda da 'yan sintiri sannan aka iya tankwara mutane aka cire tankunan.
Ba wani bayani daga karamar hukuma kamar mulkin soja bayan juyin mulki.
Nawa aka sayar da su? Babu wanda ya sani. Wa aka yi wa gwanjon su? Ba wanda ya san nawa aka saka cikin asusun karamar hukuma na sayar da wadannan tankuna? Ba wanda ya sani me aka yi da kudin da aka sayar da tankunan. Babu wani aiki takamaimai da aka yi da su sai dai jita -jita da ana tsammani.
Wannan cire tankuna na ruwa har yanzu yana bata wa mutanen karamar hukumar Kaita rai. Suna kuma jiran ranar sakamakon da za a kyale su su fadi ra'ayinsu.
MASARA, MARAR KYAU
A wani lokaci a baya gwamnatin jihar Katsina ta bai wa kananan hukumomi kudi domin su sayi masara su raba wa mutanen yankunansu.
Wata masara da ta rika yawo a Social Media mai tsiro da hunhuna, wadda aka yi ta zagin gwamnatin jiha a kanta.
Wannan masara ana zargin wadda aka saya ce don a bai wa mutanen karamar hukumar Kaita ce.
Jaridun Katsina Times sun yi magana da mutanen yankin da daman gaske da suka tabbatar masu da cewa wannan masarar Kaita aka kawo ta, wadda aka ce kowane buhu yana da tiya 32 mai makon 40.
Kuma da farko aka ce duk mai so sai ya ba da Naira 100. Jama'a suka ki saye saboda rashin kyanta bata. An tabbatar da duk wanda ya yi kuskuren cin ta, za ta iya yi masa illa.
Wa ya yi kwangilar sawo ta a Kaita? Duk iya bincikenmu ya tabbatar mana da cewa shugaban karamar hukumar ne kawai ya san wa yaba kudi ya sawo ta.
Bincikenmu ya gano masarar nan dai zubar da ita aka rika yi domin ba yadda za a iya sarrafa ta.
Katsina Times ta gano wanda da aka yi niyyar ba shi kwangilar kawo masar, amma aka hana shi aka ba shi hakuri da dan abin hasafi.
Wannan mummunar masara, Injiniya Bello Lawal kawai ya san wa ya yi kwangilar kawo ta.
Mutanen Kaita sun amfana ne kawai da shinkafa wadda gwamnatin jiha ta bayar da ita a raba a kananan hukumomi.
SU WAYE MANYAN 'YAN KWAGILAR KAITA
Binciken jaridun Katsina Times ya tabbatar mana cewa mutane biyu aka fi bai wa duk wata kwangila mai tsoka a karamar hukumar.
Daya bincikenmu ya tabbatar kanen shugaban karamar hukumar ne uwa daya uba daya, kuma kowace kwangilar akwai bukatar binciken musamman na kwakwaf a kan aikin da yawan kudin da aka yi aikin.
Misalin wasu daga cikin ayyukan sune katange makarantar Firamare ta garin 'Yandaki da katange makarantar Firamare ta garin Dankaba da aikin Allemi Sabo da aka yi.
Daya dan kwangilar da akan ba aiki wani na hannun daman shugaban karamar hukumar ne, wanda shi kuma yana ba shi aiki da sunan aikin da za a yi kai tsaye ne ba kwangila ba.
Shi ma mafi yawan ayyukan suna bukatar a binciki yawan kudin da kuma yadda aka yi su.
Misalin wasu ayyukan da aka bai wa wannan na kusa da shi akwai gyara wani rufi da ake kira ginin ofis din RUWASSA na Kaita da cikon wani rami a Matsai. Dukkanin aikin farashin da aka yi ya fi na a bayar da aikin a kwangilance nesa ba kusa ba, kamar yadda binciken numu ya gano.
FILAYE DA GIDAN 'YAN SANDA
Gwamnatin Katsina ta fitar da shelar hana sayar da filaye a kasuwanni da wasu wurare a kananan hukumomi, amma bincikenmu ya gano akwai kwakwkwaran zargin ana bin ta karkashin kasa ana sayar da filaye a kasuwar Kagadama, wanda yin hakan ya saba wa umurnin da gwamnatin jiha ta bayar, in ji wasu mijiyoyinmu.
Jaridun Katsina Times ta gano wani gida da 'yan sanda kan zauna, wanda sukan taimaka wa tsaro a yankin Abdallawa, gidan ya yi shekaru a matsayin masaukin 'yan sanda da akan turo bakin da ba su da wajen zama, shi ma ana zargin an yi gwanjonsa da kudin da ba su taka kara sun karya ba.
TALLAFIN MILIYOYIN NAIRA
Wani Kansila daga karamar hukumar ya tabbatar wa da jaridunmu cewa kansilolin karamar hukumar sun saka hannu kan takardar amincewa na bayar da tallafin kudi ga 'yan karamar hukumar, amma suna nan suna sanya ido don sanin yaushe za a yi wannan aikin bayar da tallafin na yawan kudin da suka amince a yi.
KUDADEN ZABEN 2023
Wasu dattawan jam'iyyar APC daga karamar hukumar sun yi korafi ga jaridun Katsina Times cewa, duk Kaita ba wanda zai ce ga yadda aka yi da kudaden zaben 2023. Suka ce kudin zaben da Sanata Audu Soja ya ba da kuma na gwamnatin jiha.
Sun yi zargin shugaban karamar hukumar shi kadai ya tsara yadda aka kashe su, kuma shi kadai ya san me ya amso, me kuma ya bayar, wa da wa ya ba don hidimar Zabe?
ALAKAR SHI DA MA'AIKATA DA KANSILOLIN DA YAN SIYASA
Bincikenmu ya gano alakar da ke tsakanin shugaban karamar hukumar da ma'aikata, kansiloli da 'yan siyasa tana da tsami sosai, ko kare ba zai ci ba.
Dukkanin kansilolin babu wanda yake da cikakken ingantaccen ofis na aiki kowannen su ragaita yake. Daga cikin kansilolin akwai wanda yake kwance cikin hali na rashin lafiya yana tsananin bukatar taimako. An ce ciwon har yana gab da ya taba masa kwakwalwa.
Bincikenmu ya gano akwai 'yan siyasa da ya ware ba ya komai da su bisa zargin ba su goyi bayansa ba lokacin da ya fito neman takara.
Ba ya komai da su, duk abin alheri nasu in zai biyo ta wajen shi ba su samu, kamar yadda suka yi zargi.
ZAMA OFIS KO GANIN SHI A GIDA
Bincikenmu ya tabbatar da yana cikin ciyamomin da ba su zama ofis, kuma ba ka samun shi a gida. Don kashi 95 cikin 100 na 'yan siyasar Kaita ba su san gidansa na Katsina ba. Iyalinsa suna Kano. An ce yana yin wasu kwanakin a Katsina, wasu kuma a Kano.
SAKE TAKARA
Bincikenmu ya gano yana da sha'awar sake tsayawa takarar shugaban karamar hukumar Kaita. Na kusa da shi sun ce, zai dawo ko ana ha-maza-ha-mata, saboda ya dogara ga mutane hudu; biyu mata biyu maza.
Mazan wasu na kusa da Gwamna ne, kuma wai wai yana yi masu hidima sosai. Matan kuma daya kawar matar Gwamnan Katsina ce, yayin da dayar kuma wata babbar mata ce mai mutunci da ake jin ana shiga rigarta ce kawai.
Wadannan zarge-zarge ne da jaridun Katsina Times ba su iya tabbatar da su ba, amma suna fitowa ne daga bakin na kusa da shi.
MADUBI
Wannan kadan ne daga abin da muka gano a karamar hukumar da fatan ya zama allon karin bincike da nazari don yi wa mutanen Kaita adalci na fitar masu da dan takara wanda zai tafi tare da su.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@www.taskarlabarai.com
08057777762 07043777779
Email: newsthelinks@gmail.com