Cin Mutumcin Annabi (S) ya Jawo Zaman Fargaba a Katsina...
- Katsina City News
- 31 Jan, 2024
- 1179
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A daren Talata wayuwar garin Laraba, ne da Misalin karfe Tara saura na dare, Al'ummar Garin Alhaji Yahuza da ke da nisan Kilomita hudu daga garin Katsina suka samu kansu a cikin wani yanayi a sakamakon ɓatanci ga shugaban halitta Annabi Muhammad S.A.W, da wani mabiyin Addinin Kirista Yayi, wanda hakan ya jawo hatsaniya da tayi sanadiyar Ƙona gidan shi da Motarsa a garin na Sabon gari.
Mani Habu Abubakar da ya bayyana cin mutuncin a shafin sa na kafar facebook, yayi maganganu marasa dadi ga Annabi (S) da Addinin Musulunci da Alqur'ani da sauran Sahabban Annabi (S) ko da yake wani daga cikin makusantan Mani Habu Abubakar ya bayyana wa jaridun Katsina Times cewa, ya samu matsala da Account din nasa na facebook, saidai a zantawar mu da mutanen garin daban-daban sun sheda mana cewa ba yau ya saba maganganun ba, saidai na yau sune suka fi muni.
Suka ce ko bayan da yayi Posting din, wani daga cikin 'yan garin yayi mashi Kwamen (Comment) da cewa "haba wane a matsayin ka na babban mutum kuma malamin jami'a wannan rubutun bai kamace ka ba, kai ba yaro bane". Sunce wannan maganar ita ta sanya yaje ya cire Post din da yayi ya canza maganar da wata wadda batakai wannan muni ba, amma duk da haka mutanen garin sun je har gidan sa sun kona gidan da motarsa ta hawa.
A halin yanzu dai wayuwar garin Laraba al'amura sun lafa a cikin garin na Alhaji Yahuza, wanda tun a daren jami'an tsaro sun cika garin domin tabbatar da Doka da Oda.
Saidai wasu sun koka da cewa jami'an Sojoji, sun farwa mutanen garin da duka babu ji babu gani, kamar yanda muka zanta da wani da aka lakaɗawa duka da shigarsa garin ba tare da yasan mike faruwa ba. Yace "Ni sana'a ta shine (Acaɓa) Express) naje cikin gari na dawo ina shigowa bakin garin namu bansan hawa ba bansan sauka ba, sai sojoji suka cigaba da buguna, har na fadi daga busa mashin din, bansan lokacin da aka janye ni ba saidai farkawa nayi naga mashin dina a gefe, sana fa ake fadimun ga abinda ya faru, anan aka kaini gida." Yace kuma lokacin da na farka naga wani kwance cikin jini, amma bansan daga ina yake ba." Inji shi.
Saidai mutanen garin sun sheda ma jaridun Katsina Times cewa Sojojin sun bigi mutane sosai wasu ma sai da aka kaisu Asibiti.
Da misalin karfe goman daren ranar ta Talata Mutanen garin suka kasa hakuri saida sukai wata 'Yar Zanga-zanga har zuwa gidan Sarkin Katsina inda suka bayyana wa masarauta halin da ake ciki.
Kwamishinan 'Yan Sanda na jihar Katsina ya ziyarci garin da tawagar jami'an tsaro ya duba garin da inda abin ya faru, basu cewa kowa komai ba, kuma basu kam kowa ba, saidai an tsaurara matakan tsaro a garin.
Garin na Alhaji Yahuza ya kasance baka iya bambance Musulmi da Kirista saboda duka Hausawa ne, Yare ɗaya, shiyasa ma ba'a taba samun wani sabani na Addini a garin ba, wannan shine ya sa mutanen garin suke da fahimtar juna, kuma sun bayyana ma wakilin mu cewa, su dai kam ba zasu taba kowa ba, babu ruwan su da kowa, amma wanda yayi shi za'aimawa. Don haka suna kira ga hukuma da ta dauki mataki saboda sunsan halin da ake ciki, kuma wanda yayi wannan batanci ma'aikacin Jami'ar Gwamnatin Tarayya ne ta FUDMA dake Dutsinma.
"Bamu jibdadin abunda Mani Habu yayi ba, bama goyon baya, munyi Allah wadai da hakan, saidai mun dauka kaddara ce mutum baya wuce kaddararsa" inji wani abokinsa da muka zanta da shi.
Ya zuwa hada wannan rahoto komai ya dawo dai-dai a garin na Sabon garin Alhaji Yahuza, kasuwanci da mu'amaloli na yau da kullum komai na tafiya babu wani hargitsi.
Hoto: Mutumin da yaci Zarafin, Mani Habu Abubakar