Ƴata tana aiki a CBN – Amma na fadi Gaskiya ne Game da komawar Wasu ofisoshin CBN Legas
- Katsina City News
- 30 Jan, 2024
- 336
Ali Ndume, Wanda shi ne Mai Tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Yace duk da cewa yana da yarinya dake aiki a babban bankin Najeriya (CBN), Amma abin da ya yi game da yunkurin tafiyar hedikwatar hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa (FAAN) da wasu ofisoshi. Babban bankin zuwa Legas shine "gaskiya".
A makon da ya Gabata, Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu ya ce Mai da wasu Ofisoshin CBN da FAAN Zuwa jihar Legas Zai haifar da koma baya Ga siyasar Bola Tinubu.
Sanatan ya yi wannan tsokaci ne biyo bayan sanarwar da aka yi a baya-bayan nan cewa za a mayar da waɗannan ofisoshin zuwa cibiyar kasuwancin Najeriya.
Ci gaban ya haifar da martani daban-daban, tare da masu ruwa da tsaki na Arewa kamar kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) da Ndume waɗanda suka yi watsi da yunƙurin.
Yayin da Doyin Okupe, Wanda tsohon mai taimaka wa Shugaban ƙasa ne, Yace kalaman Ndume na iya haifar da rikici, Sanata Sunday Karimi, Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, ya ce abokin aikinsa ya yi magana da kansa ba don majalisar dattawa ba.
Sai dai Okupe ya ja da baya daga baya yana mai cewa Sanatan Borno yana da amfani ga kasar.
Da yake magana da jaridar TheCable a yau Litinin, Ndume ya ce furucin nasa na cewa za a samu sakamakon siyasa Gaskiya ne.
Shin a wannan lokaci ya zama dole a mayar da wasu daga cikin waɗannan ma'aikatu da hukumomin Gwamnati zuwa Legas. Me yasa aka mayar da babban birnin tarayya daga Legas zuwa Abuja, ba saboda cunkoso ba.?
“Kuma tun daga wancan lokacin Legas ke kara fadada. Wannan hujjar da suke gabatarwa, cewa don inganci ne. Menene inganci? A duniyar yau inda zaku iya yin mu'amala ta hanyar lantarki, kuna iya yin taro ta hanyar zoom, ku ta WhatsApp, kuna iya canja wurin takardu ta PDF. Babu wani uzuri a wurin [yanke shawarar mayar da CBN, FAAN zuwa Legas].
“Idan muka zo batun siyasa, eh, dole ne ya haifar da sakamako domin zabar Tinubu Akayi ba naɗa shi akayi ba.
Sanatan na Borno ya bayyana Kwarin Gwiwar cewa Tinubu zai dauki matakin da ya dace kan lamarin.
“Ina APC kuma ina alfahari da APC. Ina Ɗaya daga cikin jiga-jigai masu Goyon bayan Shugaban ƙasa Tinubu,” inji shi.
"Wato Tinubu, ya san Gaskiya na fadi. Tinubu zai yi wani abu domin ya san na fadi gaskiya. Za a samu Sakamakon siyasa.
“Shin ba ku ga irin martanin da dattawan Katsina, ‘yan Arewa baki daya suka yi na adawa da wannan matakin ba. Shin ba Gaskiya ba ne cewa zai nemi kuri'un 'yan Arewa a 2027?
“Shin ba gaskiya ba ne ‘yan Arewa kuma ko ‘yan adawa ma za su ci moriyar wannan? Yanzu su [bangaren arewa] suna ce mana ‘Mun gaya muku cewa mutumin nan dan kabila ne, dubi abin da yake yi. A cikin shekara daya ya fara yunkurin cutar da arewa’.
KBC Hausa