Majalisar zartaswar jihar Katsina ta amince da Naira Biliyan 74.5 don gudanar da sabbin ayyuka tara.
- Katsina City News
- 29 Jan, 2024
- 613
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Majalisar zartaswa ta jihar Katsina ta Amince da kudi har naira biliyan saba’in da hudu domin aiwatar da sabbin ayyuka tara a cikin babban birnin jihar Katsina, don haɓaka ababen more rayuwa na birane da inganta kasuwanci a cikin birni.
Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri na Jihar Katsina Injiniya Sani Magaji Ingawa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaman majalisar zartarwa ta jihar na wannan sabuwar Shekara.
Majalisar karkashin jagorancin Gwamna Mallam Dikko Umar Radda ta gudanar da taronta ne domin tattaunawa kan muhimman ayyukan raya kasa.
Ayyukan, wanda aka tsara a karkashin shirin sabunta birane na Gwamna Dikko Radda, an ba da kwangila ga kamfanin CCECC na kasar Sin, da ake saran za'a gama aikin a cikin shekaru biyu.
Hanyoyin Tara da Za'a Fadada sun hada da,
1. Fadada hanyar Dutsinma, titin Kano, a bi ta titin Daura, sannan ya dangane da kauyen Yandaki dake karamar hukumar Kaita.
2. Aikin tagwayen hanyoyin da suka taso daga babban masallacin juma'a na Katsina ta hanyar Kofar Marusa, za su tsaya a shatale-talen WTC, da kuma wata hanyar daga Yandaki-Shinkafi zuwa Kofar Sauri, da Junction na filin jirgin sama zuwa hanyar da za ta bi ta hanyar Daura.
3. Tsawaita Tagwayen Titin daga Barhim Estate zuwa hanyar Mani, da kuma zarcewa zuwa ofishin Hukumar samar da Ruwa ta jihar Katsina da Kofar Sauri zuwa babban Masallacin juma'a na Katsina
4. Titin da ya fara daga Rafin Dadi ta zuwa tashar Sifiri ta KTSTA ya zarce zuwa Shatale-talen Ring road na hanyar Batsari, da Babban ofishin 'yansanda (CPS) zuwa Kofar Yandaka, da Babban ofishin 'yan sanda (CPS) zuwa kofar Kaura.
Kwamishinan ya jaddada cewa, za a ba da fifikon hanyoyi biyu daga cikin tara a matakin farko, tare da hanyar Kofar Soro zuwa Kofar Guga da gwamnatin da ta gabata ta amince da su, kan kudi naira biliyan talatin da takwas.
Titunan kashi na farko sun hada da hanyar Jami'ar Umaru Musa Yaradua (UMYU) zuwa Yandaki da Masallacin juma'a zuwa- Kiddies zuwa Shatale-talen WTC
An shirya fara aikin ne a watan Fabrairu. A kokarin tabbatar da gaskiya a harkokin kudi, kwamishinan kudi na jihar Bashir Tanimu Gambo ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar tana da wadatattun kudade domin zaburar da kamfanin gine-gine cikin gaggawa. Za a rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin jihar da kamfanin gine-gine don hana bambancin yanayin aikin.
Dr. Faisal Umar Kaita, kwamishinan filaye da safiyo na jihar Katsina, ya kuma bayyana cewa gwamnati na duba yadda za a gudanar da hada-hadar kudi a babbar kasuwar Fatima Baika da ke Katsina domin daidaita ayyuka da kuma ingantata yadda ya kamata.
Gwamnatin jihar ta jaddada kudirinta na kiyaye abubuwan tarihi a yayin gudanar da ayyukan.