SOJOJI SUN KUƁUTAR DA MUTANEN TASHARNAGULLE TA BATSARI
- Katsina City News
- 29 Jan, 2024
- 472
Misbahu Ahmad @Katsina Times
Jami'an tsaron soja, sun ƙwato mutanen Tasharnagulle ta ƙaramar hukumar Batsarin jihar Katsina.
Tun da asubahi ranar lahadi 28-01-2024 mazauna yammacin Batsari ke jin ƙarar harbe harbe da rugugin ƙarar manyan bindugu kamar ana yaƙin ƙasa da ƙasa, amma abun bai zo masu da mamaki ba domin dama sun ga shigar motocin jami'an sojoji a yankin.
Bayan ƙura ta nutsa sai aka sojojin sun dawo da mutanen da yawa akan motocin su, wasu ma har akan motoci masu sulke saboda ƙarancin inda za su shiga. Bincike ya tabbatar da cewa sunyi nasarar ƙwato mutane n da aka yi garkuwa da su na ƙauyen Tasharnagylle a makon jiya.
Katsina Times
Www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779 08057777762