Taron masu ruwa da tsaki a Arewa: Dakta Nastura ya miƙa saƙon ban gajiya da fatan Alheri ga daukacin masu faɗa a Ji daga Arewacin Nijeriya
- Katsina City News
- 28 Jan, 2024
- 725
Katsina Times
A sakon na Bangajiya bisa taron da ya gudana akan matsalolin tsaro, ranar 24 ga watan Janairu babban birnin tarayyar Abuja.
Shugaban Kwamitin Amintattu na (CNG) Dakta Nastura Ashir Sharif ya bayyana jin dadin sa da kuma sakon fatan Alheri ga Mahalarta taron Sarakuna, Masu Mukamai 'Yan Siyasa Dattawa da Masu ruwa da tsaki na Arewacin Nijeriya.
Dakta Nastura yace "A hakikanin gaskiya naji farin cikin kwarai da gaske yadda naga al'umma sun fito domin halartar taron Kuma suka tsaya har zuwa karshen taron duk da tsawon lokacin da aka dauka ana bayanai. Hakika wannan taro ne da ba'a tabayi ba a Najeriya la'akari da manya-manyan shugabannin da suka halarci taron. Wannan taron ya sake tabbatar min da cewa lalle Arewa tsintsiyace madaurinki daya kuma ya bayyana a gurin taron cewa Arewa a shirye take tsaf domin yakar ta'addanci da yan ta'adda."
Sharif ya kara da cewa, ya zama wajibi ya godewa Babban Bako a wannan taro wanda shine mataimakin shugaban kasar Nijeriya Sanata Kashim Shettima da ya samu wakilcin mataimakin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin tarayya Barasta Ibrahim Hassan Hadeja, da tsohon shugaban kasar mulkin soja kuma Shugaban tattaunawar Janaral Abdussalamu Abubakar GCFR a bisa jajircewar sa wajen ganin wannan taro ya wakana.
Nastura ya yabawa Mai Martaba Sarkin Musulmai, Alh. Sa'ad Abubakar II bisa ga jawabin da ya bashi karfin gwiwa matukar gaske, yace "kuma dole na kara godemasa bisa lokacinsa da ya sadaukar mana domin halartar wannan taro."
A cikin jawabinsa na Bangajiya da kuma jinjina, Dakta Nastura Ashir Shariff ya yabawa Gwamnonin Arewa inda ya bayyana su a matsayin abin Misali. Yace "A hakikanin gaskiya kun zama abin misali a kasarnan bisa yadda kuka tashi tsaye wajen yakar ta'addanci ba tare da nuna banbancin ra'ayin siyasa ba."
Yace yana fatan idan har suka cugaba da bin hanyar da suka dauko za a kawo karshen matsalolin tsaro, yace Arewa zata zauna lafiya, yace zasu bada cikakken gudumawa da goyon baya a cikin shirin.
Dakta Nastura ya yaba da mila sakon Bangajiya ga Mashawarci na Musamman akan sha'anin tsaro a Nijeriya Malam Nuhu Ribado, Babban Ministan Tsaron Nijeriya Muhammad Badaru Abubakar da Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle Muradun, da takwaransa ministan Noma Abu Kyari. Yace "Ina muku bangajiya da nuna farin cikina a fili ganin yadda kuka nuna cewa a shirye kuke wajen taimakon Arewa a fannin matsalar tsaro da harkar noma. General C.G Musa (Chief of Defence Staff) ina maka barka da gajiya."
Sakon bai tsaya a nan ba ya sake jinjina da godiya ta musamman ga tsohon gwamnan jihar Kwara kuma tsohon shugaban majalissar Sanatocin Najeriya, Sanata Dr. Abubakar Bukola Saraki bisa yadda ya nuna tunani da kwakwalwar sa wajen nemo mafita a Arewa.
Yabon bai tsaya a nan ba ya mika sakon na fatan Alheri ga Manyan jagorori a wannan yankin na Arewa mai albarka irinsu Farfesa Attahiru Jega, Gen. Dambazau, Dr. Ahmad Gumi, Dr. Nuru Khalid, Farfesa Ibrahim Maqari, Alh. Buba Galadima, Sarkin Yaki, da sauransu.
Dakta Nastura Ashir Shariff ya Kara jaddada Godiya ta musamman ga shugabancin Gamayyar Kungiyiyon Arewa karkashin jagoranci Comr. Jamilu Aliyu Charanchi bisa kyakkyawan guduri suka zo dashi wajen kawowa Arewa masalaha.
A karshe yayi fatan Alheri da neman rahama ga Dukkanin Al'ummar da suka samu halartar taron da Addu'ar zaman lafiya ga ƙasa baki daya