Gwamnatin jihar Katsina ta dukufa wajen dawo da Tattalin Arziki ta hanyar samar da Tsaro
- Katsina City News
- 26 Jan, 2024
- 465
Jamilu Hashimu Gora, M.A to Deputy Governor
Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Malam Faruk Lawal HCIB ya halarci taron shekara-Shekara karo na 21 da Kamfanin Jaridar Media Trust ya shirya mai taken; "Tsare Tsaren Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu: Masu Asara da Masu Kwasheta" Wanda ya wakana a dakin taro na Sojan Saman Nigeria NAF dake a Birnin Tarayya Abuja.
Da yake jawabi a wajen taron Wanda ya samu halartar Manyan Yan Jarida, da Yan Siyasa, da kungiyoyin Kwadago dana Al'umma, da Malam Jami'oi da sauransu, Malam Faruk Lawal yace kowa nada rawar da zai taka wajen sake farfado da tattalin arzikin kasa don haka dole ne a hada hannu don samun nasarar cigaban Kasa.
Malam Faruk Jobe ya kara da cewa Gwamnatin jihar Katsina maici yanzu ta dukufa wajen magance matsalar tsaro da ta addabi wasu sassa na jihar a matsayin wani mataki na sake farfado da tattalin arzikin yankin Arewa dama kasa baki daya.
A wajen taron an gabatar da kasidu tare da tattaunawa akan su da yin sharhi daga bakin masana tattalin arziki da manyan jami'ai da Malaman Jami'a da shuwagabannin Kungiyoyi.