HARIN ƳAN BINDIGA A BATSARI YA RUTSA DA ƊALIBAN MAKARANTAR SAKANDARE.
- Katsina City News
- 23 Jan, 2024
- 616
HARIN ƳAN BINDIGA A BATSARI YA RUTSA DA ƊALIBAN MAKARANTAR SAKANDARE.
Muazu Hassan
@ Katsina Times
Harin da ƴan bindiga suka kai ƙauyen Tavsharnagulle dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina, a ranar lahadi 21-01-2024 da misalin ƙarfe takwas na dare, ya rutsa da ɗaliban makarantar sakandiren gwamnati ta Ƴanɗaka Ruma, G.S.S Ƴanɗaka Ruma.
Kamar yadda ɗaya daga cikin iyayen yaran kuma mazaunin ƙauyen da abun ya faru ya labarta mana cewa "lallai muna cikin tashin hankali wanda ba zai musaltu ba, domin daga cikin mutanen da ɓarayin daji suka sace mana akwai yara ƴan makarantar Sakandire guda biyar waɗanda dukkan mu iyayen su ba mu da ko sisin kwabo, ballantana yadda zamu karɓo su, Wallahi abincin ma kullum sai mun nemo na sawa bakin salati, amma kwatsam sai ga wannan iftila'in ya faru akan mu"
Daga ƙarshe mutanen garin sun bayyana mana sunayen ɗaliban da harin ya rutsa da su kamar haka:
1. Maryam Umar, ƴar aji ɗaya a ƙaramar sakandire JSS1.
2. Halima Yaƙuba, ƴar aji ɗaya a ƙaramar sakandire, JSS1.
3. Asiya Umar, ƴar aji ukku a ƙaramar sakandire, JSS3.
4. Aliyu Habibu, ɗan aji ɗaya a ƙaramar sakandire, JSS1.
5. Abubakar Isha, ɗan aji ɗaya a ƙaramar sakandire, JSS1.
Dama dai wannan yanki na Batsari ya sha fama da hareharen ƴan bindiga domin ko a cikin satin da ya gabata saida ɓarayin dajin suka kai hari ƙauyen Sakijiki wanda yake baifi nisan 4km zuwa ƙauyen Tasharnagulle, inda suka kashe jami'in ɗan sandan kwantar da tarzoma guda ɗaya kuma suka raunata guda ɗaya.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 080577777762