'Yan Bindiga na Cigaba da Mamaye Ƙauyukan Karamar Hukumar Musawa
- Katsina City News
- 19 Jan, 2024
- 668
Ƴan Ta'addar Daji Na Ci Gaba Da Kai Harin Mummuƙe A Ƙauyukan Ƙaramar Hukumar Musawa
Daga Muhammad Aminu Kabir
Ɓarayin daji na ci gaba da cin karen su ba babbaka a yankunan karkara a cikin ƙaramar hukumar Musawa ta jihar Katsina, inda ko a daren jiya suka shiga wani ƙauye mai suna Rahusa suka bankama Garin wuta.
A Ɗan tsakanin nan irin wannan salon ne ɓarayin suka ɗauka ta Inda idan sun shiga gari bayan sun sace abinda suka sace tare da kisan ɗai ɗaya sai kuma su bankama gari wuta su kama gaban su.
Wannan harin ta'addanci dai ya shafi ƙauyukan dake zagaye da garin Dayi, Na-Alma, Tuge, Tsabe, Gangule, Dantulu, Gundawa, Bukkoki Diyam da sauran su.
Wani Mazaunin yankin yace yanzu ɓarayin sun giga da rana kata ma suke zuwa suna kaima jama'a hari, hari na baya bayan nan shine Garin Diyam Inda suka halaka kimanin Mutane Ukku ciki hadda wani Magidanci Mai Suna Sa'adu da sukayi ma gunduwa gunduwa, bayan nan kuma suka sake dawowa ranar Talatar nan da ta gabata inda suka bankama Garin wuta tare da ƙone masu rumbunan hatsin su.
Ko a garin Tsabe ma duk dai a ƙaramar hukumar ta Musawa sun kai farmaki tare da kashe kimanin Mutane Goma Sha Ukku banda waɗanda suka tafi dasu sai da aka bada kuɗin fansa kafin a sako su.
A cewar majiyar tamu tace su yanzu ma har basu ma son ace Dare yayi da ace suna da Iko da anyi ta zama a rana ba tare da Dare ya shiga a yankin ba, da zarar jami'an tsaro sun kai farmaki a yankin suka wuce toh fah su abun akan su zai ƙare ɓarayin zasu dinga bin su gari gari suna yadda suka ga dama.