Kuji wannan da kyau masu shaye-shaye;
- Katsina City News
- 30 Aug, 2023
- 1903
Shin kun sani cewa a yayin da ake wankin koda (dialysis), ana janyo jini daga cikin jiki ne ta jan ƙaramin tiyo (red tube) ɗin nan? Sai a bi da jinin ta na'urar wankin koda (dialysis machine) sannan a mayar da jinin cikin jikin mutum ta shudin (blue tube) ƙaramin tiyo.
Ana maimaita hakan sau da yawa cikin awa hudu, kuma a duk wannan lokacin, wanda ake ma wankin kodan na kwance a kan gado ba tare da motsi kwakkwara ba.
Ana wankin koda ɗin ne sau uku a sati, watau sau sha biyu a wata, kuma duk in za'a yi, yana ɗaukan awa hudu (4hrs). Kun ga mutum zai yi awa arba'in da huɗu (4hrs) a wata ana mishi wankin koda.
Wankin kodan nan a da ₦30,000 duk yi ɗaya, kunga sau uku a sati ₦90,000 kenan, a wata kuma ₦360,000. Wannan farashin da kenan, yanzu kuma sai ta Allah.
Ga wanda ya kasance suna da cikakken lafiyar koda, kodar mutum na yin wannan wankin da kanta akalla sau talatin da shida (36 times) a kullum ba tare da mutum ma ya sani ba.
Riga-kafi yafi magani (prevention is better than cure), in dai mutum ya damu da lafiyar kodar shi toh ya gujewa Shaye-Shaye, shan magunguna ba tare da bin ka'idar su ba, cin abincin da suke gurɓata jiki amma suna da daɗi a baki sai a dinga yawan motsa jiki.
Babban ni'imar da Allah ya mana shi ne na bamu lafiya ba tare da sai mun biya ba. Mu kuma hanyar yi mi Shi godiya shi ne kiyaye lafiyar mu ta hanyar da zamu iya. Sai mu dage da bauta ma Allah tukuru cikin godiya.
Wanda basu da lafiya Allah ya basu.
A.I.H