Iran: A Karon Farko Kwararrun Likitoci Sun Sake Hada Kan Mutum Da Wuyarsa bayan ya yankeshi
- Katsina City News
- 30 Aug, 2023
- 1812
A karon farko likitoci a kasar Iran sun sami nasarar sake hada kan wani matashi dan shekara 28 da wuyansa bayan da aka yanke dukkan jijiyoyin jinni da makokorosa da wuka. Amma lakarsa da kashin baya da suke hade da kai basu ji wani rauni ba.
Tashar talabijin ta Prestv a nan Tehran ta yi hira ta musamman da Dr. Sam Zeraatian-Nejad Davani shugaban tawagar likitocin da suka yi aikin a ya kuma bayyana cewa sun yi aikin sun kammala cikin nasara, matashin ya koma kamar yadda yake yana magana yana ji rana cin abinci da suaran ayyukan sa.
Dr Davani ya kara da cewa a saninsa wannan shi ne karin farkon da aka yi irin wannan aiki a kasar Iran tare da samun nasara tashin marasa lafiya ba tare da matsaloli ba. Ya ce an yi irin wadannan ayyuka a wasu kasashen Asia amma bayan aikin tiyatar murasa lafiya bai koma kamar yadda yake a da ba.
Likitan ya kara da cewa an yanka makokoro da jiyoyin da suke daukar jinni zuwa kai gaba dayansu, a lokacinda aka kawo masu marasa lafiyan don ha kain farko da suka yi shi ne samar da jinni daga waje wanda yake kai zuwa zuwa kwakwalwa da sauri don kada ya mutu, tare da hada jijiyoyin wuya da injin famfa jinni daga waje sannan a hankali suka kammala sauran ayyukan.