Ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Nahuta dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jahar Katsina.
- Katsina City News
- 15 Jan, 2024
- 521
@Katsina Times
Da misalin ƙarfe 11:00pm na daren ranar lahadi 14-01-2024 gungun ɓarayin daji masu satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa suka kai harin, inda suka mamaye sansanin sojojin da ke ƙauyen. Duk da tarin yawan su bai hana sojojin maida martani ba, amma da yake sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi, ɓarayin sun mamaye su, dalili kenan da yasa sojojin janyewa, inda ɓarayin suka samu damar ƙone motoci biyu a sansanin sojojin sannan suka sace wasu kayayyaki.
Sannan wasu ayarin ɓarayin sun afka garin suna harba manyan bindigu. Wani mazaunin garin ya bayyana mana cewa ɓarayin sun ta aman wuta kamar ana fasa dutsi da nakiya, inda suka kwashe kusan awa ukku suna buɗe wuta. Sun kwashe kayan shagunan garin kuma sun sace shanu fiye da hamsin da baburan hawa da sauran su.
A wani labari kuma, ɓaragin daji sun sace mata biyu ciki hadda amarya wacce bata wuce kwanan wata ba da shiga ɗaki a ƙauyen Batsarin-alhaji mai nisan 3 daga garin Batsari.
Haka ma a ƙauyen Ƙasai dake kusa dake hannun riga da ƙauyen Nahuta, ɓarayin sun kai harin ranar laraba data gabata inda suka kashe mutum ɗaya sannan suka sace mutane shida.
Dama dai ƴan bindiga sun saba kai irin waɗannan hare hare a wannan yanki na Ƙasai da Nahuta masu nisan kimanin nisan 10km daga Batsari. Domin a cikin watan da ya gabata sun kai ma manoma masu ɗibar dankali hari har suka kashe mutune ukku a yankin.