"Ku gayawa Abduljalal Runka ya shiga Taitayinshi Ni ba Sa'anshi bane" Abdulkadir Zakka
- Katsina City News
- 09 Jan, 2024
- 1107
Zaharddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Tsohon Kwamishina a Zamanin Gwamnatin Aminu Bello Masari, kuma tsohon Dan takarar Majalisar Tarayya a Jam'iyya APC a kananan Batsari, Safana da Danmusa Hon. Abdulkadir Ahamed Zakka ya gargadi Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin jihar Katsina akan ya shiga Taitayinshi bakin Rijiya ba wajen wasan Makaho bane.
Zakka yayi wannan gargadin ranar Talata rana ta biyu a wajen Taron Bita akan Noman Tumatiri da bayar da Tallafin Naira Dubu Hamsin-Hamsin ga mutane dari hudu da suka ci gajiyar shirin, wanda tsohon Dan majalisar Dokokin Tarayyar Nigeriya mai Wakiltar Kananan Hukumomin Safana, Batsari da Danmusa Hon. Ahamed Dayyabu Safana ya dauki nauyi.
Abdulkadir Ahamed Zakka yace "Bani Fada da Kowa Baba Ahamed Dayyabu Ubane kuma jigo na jam'iyyar APC mun zauna mun fahimci juna, ya fahimce ni na fahimce shi, kuma a gaban maigirma Gwamnan jihar Katsina don haka bani da matsala dashi" yace.
"Amma ba zan yadda karamin yaro ya dunga wulakanta ni akan Siyasa ba, kowa yasan irin jajircewar da mukai akan Nasarar sa, amma yau she ke kiran mu Mutanen Banza, to ku fadi masa yana cin arzikin Maigirma Gwamna da yanzu mun fara fadan" inji Zakka.
Abduljalal Haruna Runka Shine Mataimakin Kakakin Shugaban Majalisar Dokokin jihar Katsina wanda ya fito a yanki daya da tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Katsina Hon. Abdulkadir Zakka. Abdulkadir Zakka Dan Karamar hukumar Safana ne daga yankin Zakka, a yayin da Abduljalal Haruna Runka ya Fito daga garin Runka duk a karamar hukumar ta Safana.