Tsohon Dan majalisa Ya Dauki Nauyin Horas da Mutum 200 Noman Tumatar da Jarin Rainon Iri.

top-news



Zaharddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times

Alhaji Ahamed Dayyabu Safana Tsohon Dan Majalisar Wakilan Nijeriya, mai Wakiltar Kananan Hukumomin Safana, Batsari da Danmusa a jihar Katsina, shine ya dauki nauyin bada horo ga Mutum 200 maza da mata akan Noman Tumatiri da kuma basu Tallafin Naira dubu Hamsin-Hamsin ko wanne mutum daya gami da shedar bada horo (Certificate) ga Mutanen da suka fito daga kananan hukumomi uku da ya wakilta.

Irin wannan Tallafin shine karo na 15 kamar yanda wakilin tsohon Dan Majalisar ya bayyana a jawabinsa na kaddamar da fara bada horon na kwanaki biyu a Babban wajen Taro na "Star Event Arena" dake kan titin zuwa Mani a Unguwar Barhim cikin garin Katsina, a ranar Litinin.

Alhaji Kabir Dayyabu Shine Wakilin Tsohon Dan Majalisar, ya bayyana Irin jajircewar Hon. Ahamed Dayyabu ga Mutanen yankinsa, inda yace Ahamed Dayyabu A yankin Safana, Uba ne da bamu da kamarsa a Siyasa. Yace "Ko da Hon. Ahamed Dayyabu baya da Kujerar Majalisa a yanzu, yana yin abinda da ya saba tun yana saman kujerar.

Alhaji Kabir Dayyabu a cikin jawabinsa ya tabo irin yanda Ahamed Dayyabu ya bawa jam'iyyar sa ta APC gagarumar gudummawa, yace ko da Safana a koma jam'iyyar PDP a baya wannan wani dalili ne na siyasa, amma yanzu cikin APC yake Dumu dumu, shiyasa ma ya shirya karrama 'ya'yan Jam'iyyar sa da wannan shiri na Tallafi da bada horo, yace kuma shirin zai ci gaba.

Da yake tofa albarkacin bakinsa Tsohon Kwamishinan kananan hukumomi da Masarautu na jihar Katsina, Hon. Abdulkadir Ahamed Zakka ya yaba da kokarin Ahamed Dayyabu, ya ce; "Ahamed Dayyabu Ubane a wajen Kowa," kuma yanzu a tsakanin su babu wani abu ko a cikin zuciya, sun zama tsintsiya daya madauri daya, abinda ya faru a baya an manta dashi sun hadu don kishin ƙananan hukumomin su, da jihar Katsina ga baki daya.

A karshe ya yi addu'a akan neman dauwamammen zaman lafiya a yankunan Safana Danmusa da Batsari gami da bada hakuri, jaje da kuma kira ga gwamnatoci tun daga matakin kasa zuwa jiha akan kara maida hankali akan sha'anin tsaro, yace duk da yasan suna iya kokari.

Kafin fara shirin bada horon, shugaban jam'iyyar APC na Karamar hukumar Danmusa ya yabawa kokarin tsohon Dan majalisa tare da kira ga wadanda suka samu horon da su jajirce wajen ganin sun mori abinda suka koya.

Masana Kwararri akan Noman Tumatiri da adanashi sune suka gabatar da Lakca a wajen Taron, ina Dakta Bala Idris ya gabatar akan yanda ake rainon Irin Tumatiri har ya girma a kaiga dasashi zuwa nomansa da fitarsa ta hanya mai kyau da kuma kwarewa. 

Malam Hudu A.H ya gabatar da tasa Lakcar akan yanda zaka iya adana Tumatiri ba tare da ya lalace ba har na tsawon watanni, inda ya kawo hanyoyi da dama da ake bi a sarrafa Tumatirin a kuma adana shi.

A yayin da Mr. Layade A.A ET AL ya gabatar da Lakcar sa a cikin harshen Ingilishi akan yanda zaka iya kasuwancin Tumatiri a zamanance da kuma tsarin (Book Keeping) inda yayi bayanai Dalla-dalla hanyoyin da za a iya zama Attajiri ta hanyar kasuwancin Tumatiri.

Manyan baki da suka shedi gudanar da bada horon akwai Hon Aminu A. Garba Dan Majalisar wakilai a karamar hukumar Danmusa, Abdulkadir Zakka, Abba Dayyabu Safana, Shugaban Karamar hukumar Safana, Shugaban Jam'iyyar APC na Danmusa, Alhaji Kabir Dayyabu Safana, da sauransu.

NNPC Advert