An Gudanar Da Zagayen Mauludin Sayyidah Fatima (SA) A Katsina
- Katsina City News
- 06 Jan, 2024
- 554
Daga Isma'il Abubakar Idris
A yau Asabar ne 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky suka gudanar da gagarumin zagayen Maulidin Sayyidah Fatima (sa) a cikin birnin Katsina.
Zagayen, wanda ya kunshi maza da mata yara da manya, ya kayatar fiye da wanda aka saba gudanarwa a shekarun baya.
Masu zagayen sun bayyana cewa sun fito ne domin nuna murna da farin ciki da zagayowar Maulidin 'yar gatan Manzon Allah, kuma Shugabar Matan Duniya da Ƙiyama, Sayyidah Fatima (sa).
Sistoci sun fito cikin cikakkiya, kuma kammalalliyar shiga, yayin da sauran mahalarta suka caba ado da kwalliya, suna tafe cikin izza suna rera wakokin yabo ga Sayyidah Fatima (sa), tare da raba wa jama'ar da suka yi dafifi a gefen hanya kyaututtuka kala-kala.
Wani bangare na daliban makarantu, suna tafe suna taka fareti da kuma daga tutoci masu ɗauke da sunan Fatima cikin kwalliya da filawoyi koraye.
Su ma mawaƙa sun hau munbari suna waƙe 'yar Manzon Allah (S) wadda aka yi Duniya da Lahira domin Babanta.
Su kuma wani bangare na 'yan'uwa sun daga tutocin nuna goyan baya ga al'umma Palastinawa ne duk a wajen Muzaharar Mauludin Sayyidah Fatima (sa).