Tsaro: 'Yan Banga Da Zargin Karkatar da Shanun fulani a Mazoji, jahar Katsina.
- Katsina City News
- 04 Jan, 2024
- 1077
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, @Katsina Times
Yayin da gwamnatin Katsina ke kokarin bambance fulanin kirki da kuma miyagu domin samar da zaman lafiya ingantacce. Ayyukan wasu yan banga a yankin mazoji karamar hukumar Matazu na kokarin mayar da hannun agogo baya a yankin.
Wasu fulani da jaridun Katsina times ta samu labarin su sunyi zargin wasu yan banga sun kore masu shanu a rafi wajen shan ruwa sun karkatar da wasu.
Fulanin da suka tabbatar da gaskiyar su, suka nufi wajen jami an tsaro domin su bayyana kansu ayi bincike na gaskiya a basu shanun su.
Fulanin sun bayyana cewa bayan jami an tsaro sun tabbatar da cewa lallai shanun su na gaskiya ne, sai suka ce suje cikin shanun da aka tara su dauki nasu.
Daya daga cikin fulanin ya fada mana cewa, shanun shi talatin da uku aka kora amma shanun sa guda Goma sha shidda kawai ya gani a wajen sojoji, kuma an zabe masu koshin da lafiya, ba an gansu ba a wajen sojoji.
Wanda ya shaida ma jaridun Katsina Times yace sojoji sun tabbatar masa iya shanun da aka kawo masu kenan.
Karamar hukumar Matazu na Ɗaya daga cikin Ƙananan Hukumomi da ke Fama da Matsalar rashin tsaro a jihar Katsina. Sai dai 'wasu fulani na Matazu sun koka akan yanda wasu 'Yan banga suke keta musu haddi ba tare da tabbatar da kuma banbance masu laifi da marasa laifi ba.
Koken da Katsina Times ta samu da wasu gungun fulani a Mazoji a Karamar hukumar ta Matazu, sun zargi, 'Yan Banga da Kore masu shanu babu gaira babu Dalili.
Kamar yanda wani da ya bukaci mu sakaya sunansa ya bayyana mana, cewa 'Yan Banga sun zo har inda yake kiwon shanunsa sun kore masa shanu guda talatin da uku 33, da Tunkiya 27, yace "abin ya faru da yamma, a washe gari na biyo sawu daga mazoji zuwa Matazu, sai na tarar da shanu 16 a maimakon 33, babu guda 17, na iske shanun a wajen sojoji, saboda da suka kora su daga nan can wajen sojoji suka isa dasu, kuma ba namu kadai suka kore ba hadda na 'yan'uwana Saniya fiye da hamsin." Ya bayyana.
"Bani tsoron kowa sai Allah, nasan shanu na ne zaluntata akai, shiyasa na tunkari sojojin kai tsaye nabi shanuna don neman hakki na ba tare da fargaba ba, kowa ya san mu a garin ya san gidan mu ya san Asalin mu kuma ansan sana'armu." Inji shi
Malamin ya kara da cewa, "a lokacin da naje wajen sojoji naga shanu guda goma sha shida, banga sauran ba, sai suka ce inje Dutsinma ko Katsina in nemi shanuna, nayi Nazarin cewa ta yaya za a dauki shanu daga Matazu a kawosu Dutsinma tunda duk Local government ce, nasan ba zasu aje su nan ba, sai nayi saurin zuwa Katsina a inda ake tara shanun a can kusa da Barikin soja na duba bangansu ba." Yace a karshe na dawo Wajen sojoji na bayyana masu cewa ni bangansu ba, sai suka ce to in fita waje."
"Kuma ni abinda yasa ban je Dutsinma ba, saboda duka shanun da suke zuwa su koro mana, na 'yan garin mu Katsina suke kaisu kuma da naje Katsina naga na wasu, nawa ne kawai bangani ba. Bani ni kadai ba akwai 'yan uwana da shanunsu 25 suka bace". Injishi
An dade ana zarge-zarge akan Ayyukan wasu 'Yan Banga a yankunan da ke fama da Matsalar tsaro da kama mutanen da basu ji ba basu gani ba, su kashe ko su kwace Dukiyar su, a Kauyen Turare dake Karamar hukumar Dutsinma, ana zargin wani Danbanga da ake kira da Sani Police da yayi kaurin suna sosai, wajen irin wannan barna.
Kamar yanda ake zargi Sani Police ya zamarwa Al'umma ƙauyukan abin tsoro.
Jaridun mu sun kasa tabbatar da zargin rashin imani da akeyi ma Sani police ta bangaren shi, domin wayar shi da aka bamu bata tafiya.
mun kuma aika masa sakon rubutu a wayar shi ba amsa.
Amma mun tabbatar da yadda jama a suka tsora ta dashi, mun kuma samu labarai na tayar da hankali da aka rika dangantawa dashi.
Wannan hali na wasu bata gari daga cikin jami'an yan banga na daya daga cikin abinda ke harzuka mutanen ƙauyukan da abin ya shafa don a gaza samun daidaito da kwanciyar hankali, kamar yanda wani daga cikin mazauna yankin ya bayyana mana.
A karshe fulanin sunyi kira ga Gwamnatin jihar Katsina da ta kafa kwamitin bincike da kuma tsame bata gari da suke haddasa fitina da kwashe dukiyar Al'umma da sunan kwato shanun sata alhali ba na satar bane.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762