Shekaru (4) Da Kisan Janar Qasem Sulaimani
- Katsina City News
- 04 Jan, 2024
- 519
A Rana Mai Kamar Ta Yau Ga 3 Ga Watan Junairu 2020 A ka kashe Janar Qasem Soleimani na Iran a wani harin da Amurka ta kai kusa da filin jirgin sama na Baghdad, wanda ya haifar da damuwar duniya game da yiwuwar rikici da makami.
A ranar 3 ga watan Janairun 2020, wani harin da jirgin Amurka mara matuki ta kai ya kashe Janar Qasem Soleimani, wani Manjo Janar na Iran a filin jirgin saman Baghdad.
Jirgin mara matuki dai ya kai hari tare da kashe Soleimani a lokacin da yake kan hanyarsa ta ganawa da firaministan Iraki Adil Abdul-Mahdi a Bagadaza.
Soleimani ya kasance kwamandan rundunar Quds, daya daga cikin rassa biyar na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC), kuma an dauke shi a matsayin mutum na biyu mafi karfi a Iran, wanda ke karkashin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ali Khamenei.
An kashe 'yan kasar Iraki biyar da wasu 'yan kasar Iran hudu tare da Soleimani, ciki har da mataimakin shugaban kungiyar Popular Mobilisation Forces (PMF) da kuma kwamandan mayakan Kata'ib Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran, Abu Mahdi al-Muhandis - mutumin da aka ayyana a matsayin dan ta'ad*da.
Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce Soleimani da sojojinsa ne ke da alhakin mutuwar daruruwan Amurkawa da sojojin kawance da kuma jikkata wasu dubbai.
Tasirin Soleimani a Gabas ta Tsakiya
Janar Qasem Soleimani da ke zama babban kwamandan dakarun juyin juya halin musulunci na Iran, ya shiga kungiya ta baradan juyin juya hali ne, tun a shekarar alifa da dari tara da saba'in da biyu, karkashin jagorancin Ayotullah Khomeni. Irin bajintar da yai ta nunawa a rundunar, musamman a yakin da aka kwashi shekaru goma ana gwabzawa da gwamnatin Iraqi karkashin jagorancin Saddam Hussein, ya ba shi damar samun karin girma, har ta kai shi ga zama jagoran dakarun kundunbala da ake kira “Baradan Qudus” a shekarar alif da dari tara da casa'in. Rundunar da ke ikirarin zama cikin shiri don kwato birnin Qudus mai alfarma daga mamayar Isra'ila.
Nasarar da yayi wajen kafa kungiyoyin fafutuka mabanbanta a Iraki, wadanda su kai ta gwagwarmaya da hada baki da ake zargin yayi tayi wajen musayan bayanan sirri da kasashen ketare, musammama kasar Amurka wacce ta kasheshi daga karshe, ya kai ga mamaye kasar Iraqi da tunbuke gwamnatin Saddam ta hanyar rataya.
Nasarar da yayi da yin damara ga kungiyoyin 'yan Shi'a a kasashen ketare, kamar irin su Hezbollah a Labanan, wacce a shekarar 2003 ta gwabza yaki da Isra'ila aka tsagaita wuta bayan anyi kare jini biri jini, da kuma Kungiyar Ansarullah ta 'yan Houthi a kasar Yemen, wacce ta mamaye Yemen ta kuma damawa Saudiya da kawayenta lissafi, dama kungiyar Hashdul Sha'abi a Iraqi da Siriya, wacce tai nasarar karya lagon kungiyar IS, tare da hadin guiwa da Amurka wacce ya saba kira da babbar shedaniyar duniya, duk sun sanya masharhanta da jaridun kasa da kasa na kiransa “Kaura ja yaki na kasar” wanda yayi nasarar da tarin ofisoshin jakadanci da jami'an leken asiri suka gaza cimma.
Kasheshi da Amurka tayi dai, inji masharhanata, zai bar gagarimin gibi a kasar Iran da zai yi wuya a cikeshi kwana kusa, a yayin da kasashen da ke zargin yana musu katsalandan a yankin ke zuba ruwa a kasa suna sha, don murnar uwargijiyarsu Amurka ta raba su da alakakai.
Ya mutu yana da shekaru 62 a Duniya.