Babu iyaka ko bin doka a hare-harenmu idan Isra'ila ta kawo mana yaƙi - Hassan Nasarallah
- Katsina City News
- 03 Jan, 2024
- 679
A jawabin da ya gabatar kai-tsaye a gidan talbijin din Lebanon, shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Rasrallah ya mika sakon ta'aziyya ga kungiyar Hamas kan mutuwar mataimakin shugabanta a Lebanon, Saleh Al-Arouri, inda ya ce kisansa "babban hadari ne".
Ga kaɗan daga cikin muhimman batutuwan da ya taɓo a jawabin nasa:
Ya ce idan aka kuskura aka kaddamar da yaki kan Lebanon to za su fafata yaƙin da "ba shi da iyaka balle wat doka"
Nasrallah ya yi ikirarin matakin gaggawa da Hezbollah ta dauka ranar 8 ga watan Oktoba, da barin wuta a iyakokinta, ya taka wa hare-haren bama-bamai da Isra'ila ta yi nufin kai wa birki
Ya kara da cewa, shi ne karon farko da hakan ta faru tun shekarar 2006; lokacin yakin Lebanon, kuma Isra'ila za ta yi da-na-sani
Nasrallah ya sha alwashin daukar fansa, kuma ya ce kungiyarsa za ta mayar da martani matukar Isra'ila ta kaddamar da yaki a Lebanon
Ya kuma jinjina wa 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen kan matakin da suka dauka na kai wa jiragen ruwa da ke ketara Tekun Maliya hari
Ya bayyana Al-Arouri da ''jajirtaccen shugaba'', kuma harin Isra'ila na yankan kauna ne ya kashe shi