Yan bindiga sun sace mai jego da jinjirinta a yankin Batsari
- Katsina City News
- 28 Aug, 2023
- 957
Misbahu Ahmad
@ katsina times
A daren ranar alhamis 24-08-2023 ƴan bindiga ɗauke da miyagun makamai suka kai harin ƙauyen Gobirawa dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun ɗauki wata mai jego da jinjirinta inda suka buƙaci ta ajiye jarinrin amma ta ƙi, bayan sun tafi da ita sai suka ƙwace jaririn suka jefar dashi suka tafi da ita.
Wani da yake ɓoye a cikin jeji domin ya tsira daga harin nasu, yaji kukan jariri, sai ya ruga ya sanar ma mutanen abunda ke faruwa. lokacin da sukaje wajen jinjirin sai suka taradda shi yana ta sheƙa barci. nan take a ɗauko shi aka hannunta shi ga wata mai shayarwa domin ta cigaba da shayar da shi.
Har zuwa rubuta wannan rohoton uwar tana hannun su, baa sake jin ɗuriyarta ba.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai
All in All social media platforms
07043777779 08057777762