MAKAMA GARBA TUKUR IDRIS: MUHIMMIYAR KYAUTA GA JAMA'AR GUNDUMAR BAKORI
- Katsina City News
- 30 Dec, 2023
- 832
@ Katsina Times
Watanni bayan naɗin da Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya yi wa Makama Alhaji Garba Tukur Idris a matsayin Hakimin Gundumar Bakori a masarautar Katsina biyo bayan sauke ɗan'uwansa, an shaidi wadata mai ɗorewa da samar da zaman lafiya mai inganci, ingantuwar tsaro, haɓaka tattalin arziƙin da kyautatuwar zamantakewa a tsakanin jama'a da bunƙasa jari a tsakanin 'yan kasuwa.
Da yake ba haye ya yi wa mukamin ba, Alhaji Garba dan gado ne, Mahaifinsa Dakta Tukur Idris ya yi shekara 29 a kan karagar Hakimcin Gundumar Bakori, kafin a nada kaninsa Alhaji Sule Idris, wanda kamun ludayinsa ya haifar da gagarumin canji a shekara guda.
Iyalan wannan zuriyya mai albarka sun fito ne daga tsatson Fulani Iya Nadabo, wadanda suke jagorantar jama'a a yankunan Bakori, Kankara, Ketare, Tsiga zuwa Danja tsawon shekaru masu yawa. Rubutattun bayanai da ke hannun Gwamnati da masarautar Katsina sun tabbatar da kyakkyawan tarihin yadda zuriyyar wannan gidan suka tafiyar da jagoranci tun kafin da bayan zuwan Turawan mulkin-mallaka.
Da yake Hausawa sun ce, Barewa ba ta gudu, danta ya yi rarrafe, a nasa bangaren, sunan Makama, Hakimin Bakori, Garba Tukur Idris ya yi tambari a matsayin mutum mai ilimi, kwazo, gaskiya da rikon amana, a aikin Gwamnati da ya yi na sama da shekaru 20, musamman a hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC, inda ya yi ayyuka daban-daban har zuwa matsayinsa na Kwamishinan Yaki da Cin Hanci da Rashawa (RACC) a Jihar Sakkwato.
Kafin a nada Alhaji Garba Idris wannan matsayin, sai da aka gudanar da cikakken binciken a kan irin bajintar da ya nuna a dukkan ayyukan da ya yi a baya wadanda ke nuna shi a matsayin magajin mahaifinsa na gaskiya, wanda mulkinsa na Gundumar Bakori ya yi matukar tasiri ga rayuwa al’ummarsa a cikin dan gajeren lokaci, musamman ta fannin ilimi, darussan Musulunci, karfafa tattalin arziki da bayar da shawarwari don ci gaban zamantakewa da tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa a gundumar.
Idan abin mu yi nutso cikin tarihi da yadda Makama Garba ya gudanar da rayuwarsa ne, cikin sauki za mu fahimci irin matakan da ya taka ta hanyar gina wannan kwakkwaran tubali domin kai Gundumar Bakori zuwa tudun mun tsira.
An haifi Garba Tukur ne a ranar 13 ga watan Mayu, 1968 a garin Bakori, kuma ya yi makarantar Firamaren Nadabo, makarantar Government Day Secondary School Bakori, sannan ya yi karatun digiri na daya da na biyu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya yi digiri na farko a Kimiyyar Siyasa a shekarar 1994, yayin da ya yi na biyu a fannin alakar kasa da kasa da diflomasiya a shekara ta 2000.
Makama Garba mutum ne mai kwanzon aiki. An ga kamun ludayinsa a lokacin da aka nada shi mataimakin daraktan ayyuka na ICPC, shugaban sashin bin diddigi da gudanarwa a hedikwatar Hukumar ICPC. Daga bisa kuma Kwamishinan Yaki da Cin Hanci da Rashawa (RACC) mai kula da jihohin Sakkwato da Kebbi.
Kwasakwasai da horon sanin makamar aiki daban-daban da ya halarta, tare da guraben aikin da ya rike sun taimaka masa waje samun kwarewa da samun gogayya, inda ya fito a matsayin kwararre kan bincike da bin diddigin ayyukan almundahana masu sarkakiya.
Kwarewarsa a kan harkokin tsaro, manufofi, dabarun jagoranci, wanda ya samu bayan ya halarci Cibiyar Nazarin Tsaro da Tsara Dabarun Mulkin ta Kasa (NISS) da Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabarun Mulki (NIPSS), sun taimaka masa wajen samar da kyakkyawan jagoranci a Gundumar Bakori.
Bugu da kari, Makama Garba yana da kwarewa sosai a kan tsaro da dabarun tafiyar da mulki da ci gaba mai dorewa a Afrika, abin da ya sa aka sa shi a Kwamitin kar-ta-kwana na yi wa Hukumar Fansho garanbawul
(Inter-Ministerial Committee of the Pension Reform Task Team a 2012 da kuma Kwamitin Shugaban Kasa na sake fasalin shirin SURE-P a shekarar 2016.
Shi memba ne a kungiyoyi daban-daban wadanda suka hada da Fellow of the Security Institute (fsi); Society for Peace Studies and Practices (MSPSP); Institute of Nuclear Materials Management, Nigeria Chapter, Environmental Management and Disaster Risk Reduction institute; Certified Institute of Auctioneers, Nigeria, da Institute of Fraud Examiners.
A kasa da watanni shida da hawansa karagar mulki aka lura da irin sauyin da Malam Garba Tukur Idris yake kawowa, tare da hawa hanyar sake fasalin Gundumar Bakori.
Tsarin tafiyar rayuwarsa cikin zuhudu da tsantseni, sun kara jawo Hankalin mutane zuwa gare shi saboda yadda ya narke a cikin mutanensa. Yana rayuwa daidai da jama'ar da yake rayuwar a cikinsu, wanda hakan ya kara jawo masa farin jini da kauna a tsakanin talakawa.
ABUBUWAN DA AKA YI
*Domin ganin an tafiyar da mulkin da kowa, ya kafa wani kwamitin magabata irin sa na farko, wanda ya kunshi masu ruwa da tsaki a Karamar Hukumar Bakori, domin taimaka masa da shawarwari kan hanyoyin da za su kawo sauyi mai dorewa a Gundumar.
*Kazalika, ya kafa kwamitoci a kan ilimi, kiwon kafiya, wayar da kan jama'a, tsaro, samar da aikin yi, noma da ciyar da tattalin arzikin jama'ar yankin gaba, da nufin share masu hawaye a kan matsalolin rayuwa da ke ci masu tuwo a kwarya.
*Ya gana da malaman addinin Musulunci, tare da shawartarsu a kan su sanya tarbiyyar addinin Musulunci da ta dace ga dukkan al'ummar da ke fadin wannan Gunduma, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da ingantacciyar tarbiyya, zaman lafiya da tsaro a yankin.
*Ya ba da shawarar ganin an kafa Cibiyar Jami'ar Karatu Daga Gida (Open University Centr) a Bakori.
*An kaddamar da kamfen na kare muhalli mai karfi musamman kan sare itatuwa da ke haifar da guguwar kwararowar hamada da sauran hadurran muhalli.
Wanda yanzu duniya baki daya ke yaki dashi.
*Irin kyakkyawan dangantakar da ke tsakaninsa da gwamnatin ta taimaka wajen kawo aikin dashen itatuwa dubu 20 don shawo kan matsalar kwararowar hamada da kuma samar da wajen hutawa a karamar hukumar Bakori, tare da samar da rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana da aka tanadar don wannan manufar.
*Kazalika, ya karfafi gwamnatin Bulgaria domin ta samar da makarantu da bayar da tallafin karatu ga wasu 'yan asalin jihar Katsina, musamman a karamar hukumar Bakori.
*Ana wani yunkuri da zai kai ga sake fasalin asibitin Bakori Comprehensive Clinic zuwa cikakken Babban Asibitin.
A ranar asabar 23 ga watan Disamba shekarar 2023 makama Garba tukur Idris ya halarci taron kungiyar daliban manyan makarantun cibiyar karamar hukumar bakori.inda daliban suka karrama shi da jinjina kokari da gudanarwar da ya kawo ma bakori a Dan tsawon zaman shi a sarautar makama.
Makama Garba Tukur yana sha'awar wasan kwallon tebur (Tennis), kuma yana da aure suna zaune cikin farin ciki da Iyalansa. Allah ya albarkarsu da 'ya'ya biyar.
Kwamitin wayar da kan jama a na gudummuwar Hakimin Bakori jahar Katsina. Karkashin jagorancin
Hajiya( Dr) Mariya I Abdullahi con