"Abincin da Gwamnati ta bamu muka saida muka Sawo Tukwanen gyara maƙabartarmu" Inji Al'ummar Tigirmis
- Katsina City News
- 28 Aug, 2023
- 729
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Mutanen Kauyen Tigirmis dake kusa da Barhim a garin Katsina sun bayyanawa wakilinmu yanda suke fama da zaizayar ƙasa a makabartunsu wanda yayi sanadiyar rumtawar kaburbura da dama.
Wani mazaunin garin Malam Ilya ya bayyana cewa "Mun rasa wanda zai taimaka mana domin gyaran makabartu, mun kai kokon bararmu ga wakilanmu da masu hannu da shuni da su kawo mana dauki, amma har ya kawo yanzu babu wanda yace wani abu." Yace "Sakamakon haka ba don bamu da bukata ba, ba kuma don bamu fama da matsin rayuwa ba, manyan mu na Unguwannin mu suka bada shawarar shinkafa da gwamnati ke rabawa da masara mu saida mu sawo Tukwane don mu gyara maƙabartarmu." Injishi
Garin na Tigirmis ba akan matsalar rumtawar kaburbura ya tsaya ba, wakilin Katsina Times yaga yanda Asibitin garin take, inda kusan komai na ginin ya lalace baya ga gara da shara da wani daga cikin mazauna garin ya shedamana cewa kullum sai an kakkabe Datti, yace a haka suke rayuwa.
A karshe sunyi kira ga Al'umma masu hannu da shuni da su taimaka masu da dan abin masarufi da kuma karin kayan gyaran makabarta duba da yanayin ruwa da ake ciki a kullum sai an samu kabari ya rufta.
Kauyen Tigirmis yana nan idan an wuce gidajen Barhim, daga kudanci.